DUMURKUL ASALINSA DA TARIHINSA ASALIN MAHAIFAR SHUGABAN KASA Buhari

0

DUMURKUL ASALINSA DA TARIHINSA
ASALIN MAHAIFAR SHUGABAN KASA Buhari

Fassara Abdurrahaman Aliyu.@taskar labarai

Daga Rahoton Umar Habibu@ weekly Trust

Kauyen Dumurkul gari ne da ke da nisan kilomita uku tsakanin sa da birnin Daura, sannan kilomita biyar daga Dumurkul zuwa Kwangwalam Iyakar kasar Nijeriya da Nijar. Wannan garin ya samo sunansa ne daga kalamar Fillanci mai nufin ” wurin zaman makiyaya ko kuma Filin yadda zango”

Dumurkul kauye ne na Fulani wanda ke da matsakaitan gidaje da ba su wuce hamsin (50) ba, da kuma kuma al’ummar da basu wuce dari shidda (600) ba, wadanda ke rayuwa irin ta Fulani, wadda ta hada da Noma da kiwo, musamman saboda albar kasar noman yankin.

Gari ne da ke da yalwantaccen tarihi na wata rijiya da ta shahara. Tarihin wanna rijiya ya samo asali ne lokacin da makiyaya ke yadda zango a garin, sai suka yanke hukuncin gina rijiya a wurin saboda Dausayi wurin. Wannan yasa suka gina rijiya wadda a duk shekara suke yada zango a wajen har wurin ya zama fitacce abun sha’awa ga kowa.

Garin ya na dauke da tsofaffin hanyoyin da suka hada garin da sauran garuruwa, sannan kuma akwai babbar hanyar gwamnatin tarayya ta Kwangwalam wadda ta ratsa garin ta raba shi biyu bangaren yamma da kuma na Gabas.

Har yau har gobe mutanen garin Dumurkul Fukani ne kuma makiyaya, a lokacin damuna suna daure dabobinsu su fada harkar noma ka’in da na’in a lokacin rani kuma wasu daga cikin su sukan fita da dabobin su kiwo a wurare masu nisa. Sauran kuma suna kula da dabobinsu (garke) a wuraren da suka kebe domin kula da su.

Garin ya na da makarantar Firamare da sakandire, wanda yaran garin ke halarta domin neman ilimi, sannan suna da wadataccen ruwan sha sama da shekaru bakwai da suka wuce, wanda aka samar daga wata rijiyar burtsatse da aka gina. A bangaren lafiya kuma suna ziyartar gariruwan da ke kusa da su ko kuma birane domin samun kulawa ta musamman a fanini lafiya.

Dagacin garin, Alhaji Muhammad Nazir Sarkin Fulanin Dumurkul ya bayyana cewa wanna gari ya samo asalin sunansa ne daga magabatan da suka fara zama gari a can baya, wanda suke zowa da dabobinsu, su yadda zango na wani dan lokaci sannan su wuce. Sannu a hankali wasu daga cikinsu suka aminta da zauna wa a wajen saboda dausayin wurin, har dai Allah ya sanya wajen ya zama gari wanda ake rayuwa a cikin sa har yanzu.

Nazir ya bayyana cewa, kakansa ya labarta masa cewa, “wani Bafullatani ne mai suna ‘Kurmeji ya fara zama a wannan yanki na Dumurkul, wanda shi asalinsa dan yankin Daura ne a shiyyar karamar hukumar Sandamu, wanda ya zo wajen ya yanke shawarar gina rijiya da zai rika ba dabobinsa ruwa. Wannan rijiya ta kasance mai tarihi a wannan garin, domin bayan ya gina rijiyar ne sai mutane suka rika amfani da ita, saboda yawan ruwanta, har ya kasance mutane suna tasoqa daga masarautar Daura suna zuwa rijiyar domin shayar da dabbobinsu.
Ya kara da cewa tarihin Kumeji da ya bayar yanzu tarihi ne da ya samu kaka da kakani wanda shi ma ya gaji sarautar Mahaifinsa ne dalilin da ya sa ya dawo garin ya tare domin cigaba da shugabantar lamurran mutane, ya kara da cewa dama tarihi haka ya ke yana shhdewa daga lokacimzuwa lokaci. Mahaifinsa ya fada masa cewa har yanzu gonakan Kurmeji suna nan kuma akwai wasu da yawa daga cikin danginsa da ke rayuwa a garin yanzu haka.”

Ita kuma wannan rijiya wadda ta assasa samuwar wannan gari ta na nan har yanzu, inda a yanzu take cikin Gonar Shugaba Buhari, wanda shi ma suna daga cikin wadanda suka fara zama garin a tun farko. In da ya bayyana cewa Adamu Bafallaje Mahaifin Buhari yana da ga cikin wadanda suka rayu a garin kuma har Allah ya yi mashi rasuwa a garin, kuka kabarinsa na nan a garin, sannan har yau gidansa na nan a Dumurkul, kusa da sabon masallacin juma’a da aka gina. A wannan kauyen har yanzuna akwai kawunnan (Rafani) Buhari guda uku da ke rayuwa a cikinsa, gidajensu na nan kusa da Sabon Masallacin juma’a.

Nazir ya gwada gidan Malam Sule Maikanti daya daga cikin Kawunnan Buhari, wanda ko da ya zo bude masllacin juma’a sai da ya taka kasa ya je gidan domin ya gaida shi saboda jiyyar da yake fama da ita. Sauran kawunnan nasa sun hada da Alhaji Usman Katuru da Alhaji Sale da Altine wanda ya na daya daga cikin masu kula da gonar Buhari.

Nazir ya bayyana cewa wannan Gari ya samu wutar lantarki ne wata bakwai da ya wuce, sunyi farin ciki da haka, sannan ya bayyana cewa har yanzu dai babbar sana’ar mutanen wannan gari ita ce noma da kiwo da, ya kara da cewa har yanzu basu yadda abin da suka gada kaka da kakanni ba. Kuma suna matukarvalfari da wannan rijiya wadda ita ce silar tarihin kafuwar wannan gari.

Kawun Buhari Malam Sule ya bayyana cewa kullun waka ya ke ya samu lokaci ya ziyarci Buhari, ya tabbatar da cewa mahaifin Buhari yana dayabdaga cikin wadanda suka assasa wannan garin, in da ya bayyana cewa bayan noma da kiwo mahaifin Buhari Dan Bafallaje shaharren Mafarauci ne, wanda gidansa kullum cike yake da namun daji da yake kamowa a wajen farauta.

Ya kara da cewa mahaifin Buhari yana na auren wata mata wadda ake kira Zulai, ta rasu tun da dadewa. Sannan mahaifin Buhari ya yi matukar kokari wajen sare itatuwan da ke wurin kafin ya gina gida saboda yadda wajen yake rukuki, a takaice dai Mahaifin Buhari jarumi ne na gwadawa a fada.

Malam Sule ya bayyana cewa Buhari mutum ne mai saukin kai wanda ya ke son mutane ba ma dangimsa kawai ba, ya bayyana jin dadinsa irin yadda ya tako ya ziyarce shi har dakinsa kuma ya yi masa addu’a, inda ya kara da cewa samun irin sa sai an tona.

Buhari yana da ‘Yar uwa kwara daya da ta rahe mashi mai suna Rakiya wadda yanzu haka take zaune a wata unguwa mai suna Kofar Baru da ke cikin garin Daura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here