ANYI GWAMNAN KATSINA DA WASU JIGA JIGAI WALIMAR FURA DA NONO

0

ANYI GWAMNAN KATSINA DA WASU JIGA JIGAI WALIMAR FURA DA NONO

Daga Sanusi Rabiu Katsina

Wani matashi da ke sana’ar sai da fura da nono a garin Daura ya bayyana yadda yasa mu karbuwa ga me da irin yadda ya ke nuna matukar soyayyar shi ga shugaban kasa Muhammad Buhari.
Matashin mai suna Salisu Abdurrahaman inkiya (Mai Fura Na Buhari Daura), ya kwashe tsawon shekaru 12 yana wannan Sana’a amma cikin ikon Allah a wannan karo ne likkafar shi ta daga.
Malam ya dai ce yasamo wannan sunan ne Mai Fura Na Buhari saboda irin yadda ya ke nuna tsantsar kaunar shi ga mai girma shugaban kasa Muhammad Buhari.
Yayin da kaunar bata tsaya nan ba har da kare muradin shi ga mi da bada abin hannun shi duk saboda shugaban kasar.
Mai Fura Na Buhari ya kara da ce wa shi ma wannan kauna kusan yataso yaganta ne acikin gidan su ga mahaifin shi yadda ya ke nuna soyayyar shi ga sabon angon na najeriya.
Haka zalika Salisun ya shirya wata gagarumar liyafa bayan sa ke lashe zaben shugaban kasa Muhammad Buhari karo na biyu, inda ya gayyaci wa su daga cikin jiga jigan jam’iyyar APC ciki har da mai ba shugaban qasa Muhammad Buhari shawara kan harkokin yada Labarai wato Malam Garba Shehu yasamu damar amsa katin gayyatar.
Bayan Malam Garba Shehu akwai kuma zababen dan majalisar tarayyar nan kuma matashin da ake alfahari da shi a garin Daura Hon,Fatihu Muhammad, da fitaccen dan siyasa Hon Musa Haro Daura kuma na hannun damar shugaban kasa Muhammad Buhari da sauran manyan baki.
Taron liyafar shan furar dai ya dauki hankali matuka musamman yadda wa su manyan muqarraban shugaban kasa su ka halaraci taron, wanda dayawa lokacin da Salisu abdurrahaman yafara bayyana irin so a tsakin shi da shugaba Buhari kamar wahala kawai ya ke yi, amma daga bisani nasara ta sa me shi.
Salisu ya tabbatar da karbar mabudin mota da wa su Yan canji daga na hannun damar shugaban kasa wato Musa Haro ga me da irin soyayyar shi ga mai girma shugaban qasa Muhammad Buhari, sannan yayi matukar farin ciki daya karbi irin manyan mutane da su ke tare da shugaban kasa, yadda ya bayyana abin a matsayi kamar cikin mafarki kasancewar ya da de yana nuna soyayyar shi ga mai girma shugaban kasa amma wannan karo ne Allah yasa zai zama zakaran gwajin dafi.
Daga karshe ya hori sauran matasa da su ta shi su nemi Sana’a kuma kada araina ta ko ya ta ke, sannan yayi ma mai girma gwmnan jihar katsina albishir da cewa shi ma nan bada jimawa ba zai karbi bakunci tawagar mai fura na Buhari dan liyafar shi ta musamman.

Hoto na daya Malam Garba Shehu ne, da Salisu mai fura na Buhari Daura, da wani daga cikin manyan jam’yyar APC a lokacin gabatar da walimar shan fura bayan sake samun nasarar lashe zaben shugaban kasa Muhammad Buhari a garin Daura.
Sai hoto na biyu mai girma gwamnan jihar katsina ne lokacin da ya karbi saqon Mai fura na Buhari dan jadda cewa shi ma za’a shirya ma shi ta shi walimar ta musamman nan bada jimawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here