BAMU TABA BA OBASANJO KO KWABO BA

0

BAMU TABA BA OBASANJO KO KWABO BA

Jami’ar Karatu Daga Gida (NOUN)
Fassarar Abdurrahaman Aliyu@taskar labarai

 


Jami’ar karatu daga gida (NOUN) ta bayyana cewa ba ta biyan tsohon shugaban kasa Obasanjo ko kwandala kan aikin da yake a jimi’ar na daya daga cikin masu horaswa.

Jami’ar ta bayyana mamakinta bayan da taga wani labari da ya fito daga wata jarida ta kasar nan wadda ke bayyana cewa wai tsohon shugaban kasar ya na koyarwa a jami’ar karatu daga gida (NOUN) akan albashin dubu araba’in (40,000).

Daraktan yada labarai na Jami’ar Malam Ibrahim Sheme, ya bayyana haka ne a taron manema labarai da shugaban jami’ar Farfesa Abdalla Uba Adamu ya shirya a ranar talata domin gudanar da shirye-shiryen bikin Yaye dalibai karo na takwas da jami’ar zata gudanar a ranar asabar din nan mai zowa.

Sheme ya rawaito baban maga takardar jami’ar Mr Felix I. Edoka ya na bayyana cewa, “Suna bayar da cikakkiyar dama ga duk wasu gidajen kafafen sadarwa, kuma suna kara masu kwarin guiwar su tabbatar duk labarai da rohotannin da za su bada su zama ingantattu masu gamsarwa.

Ya kara da cewa, shugaban makatantar Farfesa Abdalla Uba Adamu ya yi wa ‘yan jarida da sauran ma’aikatan makarantar bayanin cewa takardar daukar aikin da suka ba tsohon shugaban kasa Obasanjo, tare da sauran duk wanda suka dauka irin aikin da suka dauke shi akwai bayanin abin da hukumar makarantar zata rika biyan kowanensu.

See also  Gwamantin Taraiyya Zata Samar Da Motoci Sama Da Dubu 11 domin Domin Saukaka Sufuri

Amma lokacin da tsohon shugaban kasar ya maido takardar amincewa domin gudanar da aikin ya bayana cewa zai yi aikin ne a matsayin gudumuwa, wato kyauta ba tare da an biya shi ko sisi ba.”

Ya tabbatar da cewa Farfesa Abdalla Uba Adamu bai taba ambatar cewa Obasanjo yana amasar wani abu ko zai amshi wani abu ba a matsayin albashin aikin da yake gudanarwa. Sai ma ya yi masa jinjina musamman saboda yadda tsohon shugaban kasar ya bada lokacin sa mai muhimmanci wajen yin aiki a cibiyar karatu ta jami’ar dake garin Abeokuta a jihar Ogun a matsayin mai horaswa na wucin gadi, ba tare da biyan ko sisi ba.

Ya kara da cewa, ko saboda gaba, “yana da kyau a sani cewa, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yana aiki ne a jami’ar karatu daga gida (NOUN) a matsayin mai horaswa ba tare da biyansa ko sisin kwabo ba.

Obasanjo ya bayyana wa jami’ar cewa yana wannan aiki ne domin maida alheri da alheri, musamman saboda irin damar da Allah ya bash da kuma wadda jami’ar ta bashi a rayuwa, shi yasa ya yanke shawarar bada wannan gudumuwa a matsayin sa na tsohon shugaban kasa kuma Dattijo a cikin al’umma”.

Babbana Maga-takardan makarantar ya bayyana rashin jin dadinsu da nadama bisa ga wannan labari na cin fuska da wannan jaridar ta ja za masu.

Sa hannu
Ibrahim Sheme
Daraktan yada labarai
Jami’ar Karatu daga gida (NOUN)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here