SIYASAR JAMI’AR DUTSINMA: YADDA AKA SAMU VC BIYU CIKIN KWANAKI BIYAR A JAMI’AR FUDMA
Daga Taskar labarai
A farkon satin nan ne, jaridar Katsina Post ta bada labarin cewa, a jami’ar tarayya ta Dutsinma an nada Farfesa Aminu Dalha Kankia ya zama shugaban jam’ar, tsakiyar satin kuma jami’in hudda da jama a na jami’ar ya ba da sanarwar cewa, majalisar zartaswar jami’ar ta amince da nadin Farfesa Kutugi ya zama mai rikon kujerar VC na jami’ar sanarwar tace aikinsa zai fara daga 27/3/2019.
Taskar labarai ta yi bincike na musamman a kan me ya faru?ya aka yi haka?
Bincikenmu ya gano cewa, majalisar gudanarwar ta jami’ar da ake kira, Senet sune suka fara zama don fitar da sabon mukaddashin shugaban, kafin a shiga dakin taron mai wakilai hamsin da uku, ‘yan takara hudu ke nema/wanda daya ya janye ba ayi nisa ba don ana masa yarfen ba a ta ba ganinshi yana Sallah ba, sai ya zama saura uku sune Farfesa Of Oti da Farfesa Kankia da Farfesa Kutugi, sai musulman cikin majalisar suka shawarci daya daga cikin musulmi biyu masu takara ya janye, watau tsakanin Kutugi da Kankia, daya ya janye ma daya, sai Kutugi yace ya janye, sai duk musulman dake ciki suka tsaya matsayar zaben musulmi su kuma sauran suma sukayi shawararsu a asirce cewa su zabi nasu baki dayansu.
Da aka shiga taron senet, sai ‘yan takara biyu suka bayyana,/Farfesa Kankia da Farfesa Ati aka jefe kuri’a a tsakanin su/kuma kuri’a ta nuna kanta duk musulmi baki dayansu su 33 suka zabi Farfesa Kankia, wadanda ba musulmi ba su 21 suka zabi Of Ati.
Don haka sai majalisar senet ta bada sunan Farfesa Dalha Kankia a matsayin zabin Senate na jami’a a mukamin mukaddashin shugaban jami’a ga majalisar gudanarwa ta jami’ar, wadda Dakta Marliya ita ce shugaba.
Su kuma ‘yan majalisar gudanarwa da suka zauna sai suka ce, zabin Farfesa Kankia bai dace ba, saboda jiharsu, daya garinsu daya, gidansu daya da rijistara na jami’ar.
Don haka, senet suje su sake zabe, kuma in za a sake zaben, wadanda suka tsaya da farko ban da su, sai dai wasu daban su fito don haka sai duk membobin na senet suka ce, saboda dattakun da Farfesa Kutugi ya nuna a takarar farko a kyale shi ya fito ba tare da wata hamayya ba.
Wasu membobin senet sun kawo wasu rauni da Farfesa Kutugi ke da shi, irinsu cewa, bai goge ba a iya harshen turanci gangariya irin wanda za a ce lallai malamin jami’a ne, yana da rauni wajen daukar matsaya, kuma jami’ar tayi masa girma, saboda rauninsa na jagorancin shugaban ci. Amma aka yabe shi yana da gaskiya, da dattaku, da jajircewa a aiki, membobin suka zartas cewa a kawo sunansa a wajen taron.
Senet na hadowa a karo na biyu, cikin mintuna 25 suka yanke shawara akan a bada sunansa ga majalisar gudanarwa ta jami’ar.
Majalisar na zama, suka duba takardunsa, suka amince da nadin sa a matsayin sabon mukaddashin shugaban jami’ar FUDMA Wanda zai fara aiki daga 27/3/2019