SAKATAREN GWAMNATIN KATSINA ZAI KOMA MAKARANTA

0
2159

SAKATAREN GWAMNATIN KATSINA ZAI KOMA MAKARANTA

Daga Taskar labarai

Alhaji Mustafa Muhammad Inuwa

sakataren gwamnatin jihar Katsina zai koma makaranta don karatun digrinsa na uku (Phd) wanda zai bashi matsayin dakta.

Wani bincike da Taskar labarai tayi a kan daliban da suka cika fom na shiga jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua don karatun na digri na uku, ta ga harda fom wanda Alhaji Mustafa Inuwa ya cika yana neman a bashi gurbin karatun zama dalibi don karanta digrinsa na uku, a sabbin daliban da za a dauka na shekarar 2019.

Taskar labarai ta gano a karshen watan Maris za a tantance masu bukatar zama daliban digiri na uku ciki harda Alhaji Mustafa Inuwa, bayan tantancewa za a duba yiyuwar cancantar a basu gurbin karatun ko a hana su.

Shi dai Alhaji Mustafa Inuwa shi ne Dan siyasa mafi karfi a siyasar jhar Katsina, kuma an dade ana kiransa da dakta.

Taskar labarai ta gano kwazonsa ga aiki da mukaman da ya rike a baya, ciki harda kwamishinan ilmi ta sanya an sha bashi mukamin Dakta na girmamawa, yanzu kuma zaya fara karatun Dakta na ilmi
________________________________________________
Taskar labarai, jarida ce mai zaman kanta da ke bisa yanar gizo a shafin www.taskarlabarai.com da kuma duk sauran shafukan sada zumunta na Facebook,YouTube da Instagram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here