SARKIN DAURA YA SAKI MATARSA HAJIYA AISHA

0
7859

SARKIN DAURA YA SAKI MATARSA HAJIYA AISHA

Daga Taskar labarai

Mai martaba sarkin Daura Alhaji(Dr) Umar Faruk Umar CON ya rabu da matarsa Hajiya Aisha Umar Farouk Umar, wadda ita ce kamar amarya a gidan.

Sarkin ya kuma auri wata yarinya yar Kano amma yar asalin kasar Nijar a ranar jummar da ta gabata.

Editocin jaridar Taskar labarai sun ga wasu bidiyo da tsohuwar matar ta sarkin Faura, Hajia Aisha tayi da waya, bidiyon wnda Taskar labarai ta tabbatar da ingancinsata na’urorin tabbatarwa.

A bidiyon kamar yadda Taskar labarai ta gani, Hajia Aisha na cewaa taya su murna yau mai martaba sarkin Daura ya karo mata abokiyar zama.

A bidiyon farko Hajia Aisha na cewa ta san sarki mai adalci ne, zai masu adalci, kuma abin da yayi ba laifi bane, sunnar manzon Allah(SAW) ce.

A wani bidiyo an ga Hajia Aisha na rawar disko na murnar karin auren, a kuma wani bidiyon ta na kara bayyana rashin damuwarta a kan auren.

Kwatsam kuma sai ga wani rubutu maras dadi da editocin jaridar suka gani, wanda basu tabbatar da wa yayi shi ba.

Bincike na Taskar labarai ya tabbatar da cewa, wasu dalilai wadanda mai martaba ya bar wa kansa sai na kusa da shi ya sanya ya saki matarsa Hajia Aisha saki daya a lokacin da ita bata ma kasar tana waje.

Sarkin na Daura ya auri Aisha a aure na mutunci wanda maganarsa ta watsu a kasar nan, kuma suna da haihuwar diya mace kwara daya a tsakaninsu.

Kafin ta aure shi, ta fara auren sanata Bello Hayatu Gwarzo, wani hamshakin attajiri Dan siyasa dake Kano, Wanda suna da ‘ya’ya a tsakanin su, kuma suna fafatawa a kotu da shi akan kula da dan dake tsakanin su.

Hajia Aisha diyace ga Alhaji Isah Katsina, daya daga cikin dattawan jihar Katsina.
________________________________________________
Jaridar Taskar labarai jarida ce, mai cikakkiyar rijista dake bisa shafin yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta na Facebook, Twitter, Instagram, da YouTube da layin whatsapp na 07043777779.
Rika bin shafukanmu don jin bincike na musamman da sahihan labaraida nishadantarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here