DARASI DAGA LITTAFIN DADASARE: ALLAH KAN CIKA MA BAWA GURINSA KOMAI TSAWO LOKACI

0

DARASI DAGA LITTAFIN DADASARE: ALLAH KAN CIKA MA BAWA GURINSA KOMAI TSAWO LOKACI

Daga Danjuma Katsina

Hajiya Dadasare Abdullahi marubuciya, malamar lafiya ‘yar jaridata farko tun lokacin mulkin Turawa wadda aka haifa a tsakanin 1918.

A shekarar 1975 ta rubuta littafin tarihin rayuwarta mai suna ‘IT CAN NOW BE TOLD’, tayi kokarin littafin ya fito tun tana da rai amma har a shakarar1984 data rasu ba a buga littafin ba.

Duk kuwa da cewa tayi aiki da kuma alaka da kamfanin buga littattafai na farko a Nijeriya, watau NNPC Zaria. Bayan rasuwarta, ‘yar da ta rika Hajiya Aisha Dikko wata ‘yar asalin Daura ta jihar Katsina.

Tayi kokarin ganin ko littafin za a buga shi a cika ma Dadasare gurinta na rayuwa, abin ya ci tura, rubutun ma ya bace suka rungumi kaddara.

Kamar shekaru biyar da suka wuce, wata mai karatun Digri na uku a jami’ar Bayaro ta Kano mai suna Aliya Adamu Ahmad, ta fara binciken ina zata samu rubutun?

Kamar yadda Allah ya kaddara, sai wani malaminta baturen Ingila mai suna Murry Last, shima ya fara binciken ko za a samu rubutun a wajen wani da ya san Dadasare.
Kwatsam sai aka samu rubutun a wajen wata jikar kawar Dadasare a Amurka.

Murray Last ya kai rubutun dakin adana rubutun tarihi na dakin karatun a Landon, sannan ya aiko wa da dalibarsa kwafi daya.

Dakta Aliya na ajiye da kwafin littafin, sai da labari yayi labari ita da malam Ibrahim Sheme shugaban sashen sadarwa na budaddiyar jami’a ( NOUN) shi ma kuma ya dau nauyin nazarin littafin da buga shi.

A 30/3/2019 aka buga littafin, ya kuma fita kasuwa shekaru 44 da rubuta littafin ya kuma fito shekaru 35 bayan rasuwar marubuciyar.

Littafi ne, mai dadin karatu da darasin rayuwa da dinbin ilmi a cikinsa.ta bada labarin yadda wani bature ingila ,jami i a turawan dake Mulkin kasar nan ya Sanya aka Sato ta, ya ajiye ta kamar matarsa.da sauran labarai masu ban tausayi.da yadda ta rike imaninta na musulma.duk da dangantakarta da turawa.
Ga mai bukatar littafin a Katsina zai iya samunsa a Matasa Media links dake Kofar Kaura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here