AL’AJABI Ƙaramin yaro ya cire makuden kudade ba tare da katin Atm ba !

0

AL’AJABI Ƙaramin yaro ya cire makuden kudade ba tare da katin Atm ba
!
!
!
!
Wani abin mamaki da ya faru a jiya Talata 9 ga watan Afrilu, a wani injin cire kudi (ATM), na wani banki a kusa da gidan rediyon Najeriya, da ke Dugbe, cikin jihar Ibadan, inda aka kama wani matashin yaro yana cire kudi a injin cire kudin ba tare da amfani da katin cire kudi ba.
A lokacin da ya ke magana da ma’aikatan gidan rediyon Najeriya, Morufu ya ce ya na da wata lamba da ya ke amfani da ita a duk lokacin da ya ke bukatar kudi zai je injin cire kudi (ATM) ya saka zai ciri iya kudin da ya ke bukata ya tafi abinshi.
Asirin Morufu ya tonu ne a dai dai lokacin da wani mutumi ya zo wucewa ta gaban bankin, ya ga Morufu da makudan kudade a gaban injin cire kudin.
Mutumin ya bayyana cewa lokacin da ya ga Morufu ya ji zargi ya shiga ranshi, ganin kayan da ke jikin shi sunyi datti, sannan kuma ga yarinta a tattare da shi, kuma ya ga ya na cire kudi masu yawa a inji. Mutumin ya ce tun lokacin ya ji ranshi ya kasa aminta da yaron.
A karshe dai an mika yaron zuwa ga hukumar ‘yan sanda ta jihar domin gabatar da bincike akan shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here