KASHE NAIRA BILYAN UKU DON KAMA ASSANGE

0

KASHE NAIRA BILYAN UKU DON KAMA ASSANGE

Daga Taskar labarai.

An kama Julies Assange mutumin nan da yayi suna a duniya wajen sato bayanan asiran gwamnatocin kasashe yana tona wa ta watsa su a wani shafinsa na yanar gizo mai suna ‘Wikileaks’.

Assange ya tona da watsa asiran manyan kasashen Turai kuma aka rasa kan wace doka za a kama shi da ita.

A kasar Sweden aka fara nemansa bisa zargin cewa wata mata ta ce ya neme ta da karfi, da yazo London aka kama shi bisa waccan tuhumaar ta kasar Sweden, aka tsare shi aka kai shi kotu aka bada belin sa, ana bada Belinsa a 2012, sai ya nemi mafaka a ofishin jakadancin kasar Ekwado, inda yake boye har jiya da aka sake kama shi.

Ministan cikin gida na kasar Burtaniya yace, kasar ta kashe fam miliyan Goma sha uku don kokarin ganin sun kama Assange, wanda kudin yafi naira bilyan uku.

Ya fadi haka ne, ga majalisar wakilai ta kasar da yaje bayar da bahasin kama Assange. ‘Yan majalisar sun tambaye shi, “nawa aka kashe kafin a samu nasarar kama shi?” Yace ‘yan sandan ingila da sauran hukumomin tsaro sun kashe fam miliyan goma sha uku kafin suyi nasarar kama shi.

Assange ya kware wajen shiga yanar gizo ya kuma sato bayanan kasasashe ya dora shi a shafin sa na yanar Gizo.

Kasashe da yawa suna jin haushin abin da ya ke, ciki harda Najeriya. Babbar kasar da yafi yima illa itace kasar Amurka, wadda yanzu take neman Ingila ta mika mata shi.

Assange ya rika tona mata asiran da suka kara zubar mata da kima a duniya. Amurka tana son tuhumarsa da laifin satar mata bayanai da kuma watsa su ba bisa kaida ba.

babbar matsalar da Assange yake fuskanta shi ne baya da kariya ta aikin jarida, don shi ba Dan jarida bane, kuma baya cikin kungiyoyi na marubuta ko na jarida a duniya. Amma kungiyoyi kare hakkin Dan Adam dana ‘yancin fadin ra’ayi suna a bayansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here