Wani Shashe Na Masallacin FADAN ZAZZAU

0

TARIHI

Wani Shashe Na Masallacin FADAN ZAZZAU.
An Fadada Gina Shi Ne A 1830s .

An Ruwaito Cewar Wani Shahararren Magini Me Mai Suna Babban-Gwani Yai Aikin Fadada Gina Shi, Kuma Yana Aiki Da Leburori Fiye Da Mutum Dari, Kuma Da Daddare Sannan Ance Duk Sai Ya Kure Su Da Bani Bani Laka. Kuma Hatta Filasta Da Adon Zane-Zanen Dake Jikin Ginshikan Masallacin Da Kusurwoyin Ta Da Kuke Gani Duk Shi Yayi Su Cikin Ban Kaye.
Wannan Hoto An Dauke Shine Tun 1910.

Har Yau Ginin Na Nan Cikin Masallacin FADAN ZAZZAU Din.
Kuma Har Yanzu Zuriar Wannan Bawan Allah Babban Gwani Suna Nan Cikin Birnin Zaria.

Allah Ya Sanya Shi Da Sauran Magabatan Mu Suna Kyakkyawan Matsayi.

Ashe Arewa mun dade da Fasahar Injiniyancin gini Tun Kafin zuwan turawa ?
Jama’a Me Zaku Ce?
Mun Ciro daga rubutun wani da bai bayyana sunansa ba a rubutun

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here