GWAMNA YA AMINCE DA CANJIN DURBIN KATSINA?

0

GWAMNA YA AMINCE DA CANJIN DURBIN KATSINA?

Daga taskar labarai

Wani labari da Taskar labarai ta samu kuma ta bincika shi ne, maganar canjin sarautar Durbin Katsina daga jJkamshi zuwa Mani, har yanzu akwai sauran rina a kaba a cikinsa.

Taskar labarai ta ga wata takarda da sakataren masarautar Katsina ya rubuta ma sakataren gwamnatin jihar Katsina a kan, neman canza matsayin hakimin Mani, sarkin gabas zuwa Durbin Katsina kuma daya daga masu nada sarki.

Daga nan kuma sai wata takardar da take tabbatar da cewa hakimin Mani ya zama Durbi na Katsina.

Shafukan yanar gizo sun cika da hotunan hakimin Mani Wanda aka yi wa albishir na sabon Durbi yana cikin farin ciki da murna.

Wasu hotunan sun nuna yadda ake taya shi murnar samun wannan sabon matsayi. Amma abin da Taskar labarai ta gano mai girma gwamnan Katsina, sam bai amince da wannan canji ba. kamar yadda masarautar Katsina ta rubuta masa tana son tayi.

Kuma jami’an gwamnatin Katsina basu ji dadin fitar takardun guda biyu ba ga jama’a da kuma rubuta takarda ga sabon Durbin kafin amincewar gwamnan Katsina.

Wata majiya tace takarda biyu aka kai ma gwamnan ta galadima da kuma canjin Durbi sai ya amince da ta Galadima yace ta canjin dDurbi sai ya dawo yabi maganar.

Wani masanin fada ya, fadawa Taskar labarai cewa yana da wahala canjin yayi nasara, domin matsayin Durbin Katsina, matsayin daya daga cikin hudu na masu nada sarki ne.

Wanda gwamnatin jiha ke da iko kansu da nada su, don haka ba a cire su sai da wata kwakwkwarar hujja a bayyane kuma mai karfin gaske.

Masanin na sarautar yace, in aka amince da canjin, kamar an yi wa Durbi kora da hali ne, wanda sai dai ya ajiye mukaminsa na hakimci don matsayin da aka mai da shi kamar an yi masa dafkal ne.

Masanin yace, amincewa masarauta ta iya canza masu nada sarki siddan, ba karamin kutse bane ga tsarin na masarauta.

Taskar labarai na ganin yana da wahala gwamnan ya amince da wannan canjin, don haka sarautar sabon Durbin tana kasa tana dabo.

Shi dai durbin na Katsina hakimin Jikamshi.ya samu wata matsalar cikin gida ne, shi da sarkin Sullubawa hakimin Kaita da babban wansu kuma mai martaba sarkin Katsina Dr Abdulmumin Kabir Usman.

Wanda ta kai ga har an dakatar dasu, bisa zargin rashin da a da biyayya Taskar labarai, taji daga na kusa da bakunan Durbi da Sullubawa, amma bata ji daga bakin masarautar Katsina ba. Wannan ne, ya hana kawo cikakken me ya faru?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here