YADDA MASU GARKUWA DA MUTANE SUKA KASHE MIN DANA Daga Ibraheem El-Tafseer

0

YADDA MASU GARKUWA DA MUTANE SUKA KASHE MIN DANA

Daga Ibraheem El-Tafseer da Yusuf Waliy

A makon da ya gabata ne wani yaro mai kimanin shekaru 4 ya bata a garin Potiskum dake jihar Yobe, daga baya kuma sai abin ya zama ashe ba bata yaron ya yi ba, masu garkuwa da mutane ne suka dauke shi, wai sai an basu kudi Naira Miliyan 8 sannan su sake shi. A qarshe dai an kama wadanda suka yi garkuwa da yaron, amma kuma sun kashe yaron, bayan sun cire wasu sassa na jikinsa. Wakilanmu Ibraheem El-Tafseer da Yusuf Waliy sun tattauna da mahaifin yaron don jin haqiqanin abin da ya faru, ga yadda hirar tasu ta kasance;

ALMIZAN: Da farko ka gabatarwa da masu karatu sunanka.

ADO MANDIRI: Sunana Adamu Ibrahim Guga, wanda aka fi sani da Ado Mandiri Potiskum.

ALIMIZAN: Mun samu labarin yaronka ya bata, sai kuma aka ce an samu gawarsa, ko za ka mana bayanin yadda abin da faru?

ADO MANDIRI: To Yaro na mai suna Al-amin, mai shekaru 4 da wata 3, ya bata ne ranar 17 ga wannan wata na Afrilu. Da magariba ne yaron ya fita, ya zauna a kofar gida. To da muka ga shiru bai dawo ba, sai muka fara nemansa a gidajen maqwabta da gidajen masu unguwanni, har zuwa wayewar gari dai ba a samu yaro ba. Haka dai muka ci gaba da nemansa har zuwa gidajen ‘yan’uwanmu. Daga qarshe dai sai muka je muka sanar a hukumar watsa labarai ta qaramar hukumar Potiskum da gidan Rediyo aka yi ta cigiyar yaro, amma ba a same shi ba. To da daddare ina zaune a gida, sai ga wani yaro ya shigo da takarda, a jiki an rubuta Maman Haidar (Matata kenan) da kuma lambar waya a rubuce a jikin takardar. (Kwana daya da batan yaron kenan).

Da yaron ya shigo, sai ya ce ina Maman Haidar? sai nace masa ga ta nan. Sai ya ce wai gashi ta kira wannan lambar. Sai na cewa yaron waye ya turo ka da wannan takardar? Sai ya ce min yana waje. Sai nace masa to muje wajensa. Muna fita, sai muka ga babu kowa, wanda ya turo shi da takardar ya gudu. To daman a kofar gidana, akwai inda muke Sallar magariba, sannan mu yi karatu bayan mun idar da Sallah din. Bayan mun idar da Sallah, sai na nunawa ‘yan’uwa dake wajen takardar da aka turo min. Sai na yi ta qoqarin kiran lambar da aka ce na kira din, amma ba a dauka. Har sau 5 ina kira amma ba a dauka ba.

Can sai ya yi min ‘flashing’ sai na kira shi. Sai ya ce min yaronka Al-amin ya bata ko? Sai nace masa eh, sai yace to ba bata ya yi ba, mune muka dauke shi. Nace ikon Allah! To yanzu yaya za a yi? Sai yace idan kana son yaronka, sai ka bamu kudi Naira Miliyan 8. Take sai nace masa bazai yiyu ba, nace ni bazan bayar ba. Sai ya ce min wai to nawa zan basu? Sai nace ai ku ne yaro yake hanunku, don haka kune za ku fadi yadda za a yi. Sai yace wai to na basu Naira Miliyan bakwai. Sai nace ni bazan bayar ba. Wai to idan bazan yi magana ba, shi zai kashe wayarsa sai bayan kwana uku zai bude. Har yace min wai shi daga zamfara yake, shekararsa 17 yana wannan aikin. Can da daddare sai ya sake kira na, yake ce min wai a ina muka tsaya akan batun kudin da zan basu? Sai nace ni dai ina nan akan baka ta, bazan bayar da Miliyan bakwai ba. Har ya yi min barazanar zai kashe ni, ya kuma kashe yaron. Sai nace masa ai ni baza ka bani tsoro da mutuwa ba, ni fa almajirin Shaikh Ibraheem Zakzaky ne, wallahi na fi qarfin ka bani tsoro da mutuwa. Sai yace min wai ya fuskanci na fusata, wai shi mutum ne mai sauqin kai, wai ya kamata muyi magana ta nutsuwa da fahimta. Sai nace masa to yaya yake so a yi? (Duk abin da muka yi dashi a waya, ina sanar da jami’an tsaro).

Bayan mun yi ta fafatawa akan adadin kudin da zan basu, a qarshe dai suka ce na basu miliyan biyu. Yake ce min shi fa wadanda suka saka shi ya dauki wannan yaron sun san ni, kuma ya fuskanci ma cin amana aka yi min. Ya ce min kwana 4 suka yi suna tarkon yaron, sai rannan din suka samu suka dauke shi. Na ce ko ma dai menene yanzu yaro yana hanunuku, amma bazan bayar da miliyan biyu ba. Haka dai muka yi ta muhawara dashi akan adadin kudin da zan basu din, a qarshe dai sai yace wai na basu Naira dubu 50 za su saka katin waya. Sai ya fadi inda zan kai kudin, shi kuma zai je ya dauka. Da farko yace na kai kudin sabuwar Tsangaya dake kusa da Masallacin jumu’a na Tandari. Da naje na kira wayarsa a kashe, sai na qi ajiye kudin.

Can sai ya kira ni, wai ya ban kai kudin ba, nace masa naje zan kai kudin, na kira wayarka a kashe, sai na qi ajiye kudin. Sai ya ce wai na tashi da Asuba, na kai kudin kusa da wani Famfo dake kudu da gidana. Nan ma dai bai yiyu ba, yace na kai Dambuwa, yace na kai Bedu. Duk inda yace na kai kudin tsukin unguwar ta mu ne. Kuma duk anan kam bai yiyu ba. A qarshe sai ya ce na kai kudin can wata Gada dake hanyar Jos, wato Gadar Sokol. Bayan sallar Isha’i na je Gadar Sokol din, da na hau saman Gadar sai na kira shi, nace na zo Gadar ta ina zan ajiye maka kudin? Sai ya ce min na jefa kudin ta gefen hagu. Sai na jefa kudin. To daman duk abin da yake gudana tsakanina dashi, jami’an tsaro suna sane da komai.

Bayan na jefa kudin sai na kira shi, sai na ji wayarsa a kashe. Bayan wasu ‘yan mintuna kuma da na sake kira, sai wayar ta shiga. Sai na ce masa na jefa kudin. Sai ya ce min to yana zuwa, bari ya duba. Minti kadan sai ya kira ni, yace eh lallai sun ga kudin har sun dauka, don haka naje Dogon Qarfe (kan babban titin da ya ratsa cikin garin Potiskum) wai zan ga Jar mota, to yarona yana ciki, za su ajiye min shi, na je na dauke shi. Sai wadanda muka tafi dasu tare suka ce wallahi qarya suke basu zo sun dauki kudin nan ba, yaudara ce kawai. To amma dai a hakan sai muka taho Dogon Qarfen, amma muka samu babu kowa. Har lokacin doka ya shiga (wato qarfe 10:00 na dare) basu kawo yaron ba.

Idan na kira shi a waya, sai yace wai suna zuwa. To wajen qarfe 10:30 na daren sai suka je daukar kudin a inda na jefa musu, sai kawai ‘yan Sanda suka kama su anan, su biyu ne. Sai ‘yan Sandan suka kiran a waya, suka ce sun kama su nazo. Dukkansu yara ne masu qarancin shekaru. Babban shekararsa 20, dayan kuma shekararsa 16. ‘Yan Sanda suka yi ta musu tambaya akan inda yaro yake, amma suka qi fada. Da gari ya waye sai aka tafi dasu ofishin C.I.D dake garin Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe. Duk tambayoyin da aka musu akan su fadi inda suka ajiye yaro amma sun qi fada. To sai yau 29 ga watan Afrilu da muka koma Damaturu din, da ni da yayanmu Malam Bomoi, sai muka tarar an kira ‘yan’uwan yaran da aka kama din. Har da yayan mahaifinsu. To sai shi yayan mahaifin nasa, ya ja yaron suka koma gefe tare da dan sanda guda daya. Ya tambaye shi haqiqanin inda suka ajiye yaron, shi ne yace yaron sun jefa shi a wani rami a Tandari.

To sai da ni, da ‘yan Sanda da kuma shi yaron da aka kama din muka taho Potiskum, muka je ya nuna inda suka jefa yaron nawa kusa da maqabarta dake Tandari. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! (Kuka) A ‘suck away’ suka jefa shi bayan sun qwaqule idonsa, sun yanke maqogwaronsa, sun kuma yanke Azzakarinsa. Sannan suka jefa manyan duwatsu akansa bayan sun jefa shi a cikin ramin. Yace tun ranar da suka dauke yaron suka jefa shi a ramin, ka ga kenan kwanansa 13 a cikin wannan ramin. Kuma ramin a rufe yake, an liqe shi da siminti. Amma saboda tsantsar zalunci da rashin tsoron Allah, a hakan suka nemi na basu maqudan kudi. Yaron duk jikinsa ya zagwanye, a haka dai aka tattara shi aka masa sallah, aka binne shi.

ALMIZAN: To yanzu me jami’an tsaro suka ce maka game da wannan al’amari?

ADO MANDIRI: Eh to, komai dai yana hanun jami’an tsaro din. Kuma sun koma da yaron da aka kama din Damaturu, domin ci gaba da bincike.

ALMIZAN: Mun gode. Allah ya kiyaye na gaba. Ni ma Nagode.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here