SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY YA RABA KAYAN ABINCIN RAMADAN A BANA DUK DA TSAREWAR DA AKE MASA

0

SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY YA RABA KAYAN ABINCIN RAMADAN A BANA DUK DA TSAREWAR DA AKE MASA

Daga Ammar M. Rajab da Tahir Ibraheem

Kamar kowacce shekara, Shaikh Zakzaky na raba kayan abinci ga mabukata a lokacin watan Ramadan. Kuma wannan aikin ya kwashe shekaru yanayinsa. Domin duk shekara yana rabawa bayin Allah abincin da suke amfana da shi a lokacin watan Ramadan mai alfarma.

A bana ma duk da halin da azzaluman kasarnan suka sanya shi ciki tun a shekarar 2015 har zuwa yau na kashe masa ‘ya’ya da almajiransa sama da dubu da sauran yan’uwansa na jini da jikkata shi da mai dakinsa Malama Zeenatu (Ummus Shuhada) tare da kuma hana su ganin kwararrun likitocin su duba su har na tsawon kusan shekara hudu bisa zalunci. Duk da ma akwai umurnin da wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar na sakin su tare da biyansu diyya da kuma gina mai gida a duk inda yake so a arewacin Nijeriya, amma gwamnatin zalunci na Buhari tai kunnen-uwar shegu da hukuncin kotun duk da karyar suna bin dokar da su suka yi imani da ita.

A jiya Asabar 29 ga watan Sha’aban 1440 Hijiriyya wanda ya yi daidai da 04/05/2019 ne, Shaikh Zakzaky daga inda ake ci gaba da yi masa haramtacciyar tsarewa ya ba da umurnin fara raba kayan abinci ga mabukata na watan Ramadan kamar yadda ya saba yi tsawon shekaru a baya da ma tun bayan tsarewarsa. Inda ‘yan’uwan da aka kalla musu rabawar, suka cika umurni.

Abincin da aka raba sun hada da: Shinkafa, Gero, Masara, Dawa da kuma Suga da ma sauran su. Wannan rabon da Shaikh Zakzaky ke yi ba sabon abu bane ga mutanen garin Zariya da kewaye. Domin an saba yinsa.

Shaikh Zakzaky a karshe ya yi fatan alheri ga al’ummar Annabi Muhammad (S) dangane da shigowar goshin watan Ramadan mai alfarma.

-AMMAR MUHAMMAD RAJAB
TAHEER IBRAHIM

05052019

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here