SANATA ABU IBRAHIM YA BA MARA DA DA KUNYA

0

SANATA ABU IBRAHIM YA BA MARA DA DA KUNYA

daga Taskar labarai

Sanatan yankin Funtua, mai barin gado sanata Abu Ibrahim, ya baiwa mara da kunya,ya yi abi yabo da addu’a ta gari.

Sanata ne, da yana bisa kujerar yace ya hakura ya janye wasu su zo su yi tasu rawar. Kuma ya tsaya tsayin daka sai da jam’iyyarsa ta kai labari. Ana tsammanin tun da ba zai sake takara ba, ko zai juya wa jama’arsa baya.

Duk wata hidimar alheri ba wanda ya fasa, shi ne na farko da ya kai agajin gaggawa ga yan gudun hijira na yankinsa da ibtila in mahara ya auka masu.

Ana saura Kwana biyu azumi, yayi rabo na kayan azumi a garin Kankara a karamar hukumar Kankara. Wanda shi ne dan siyasa na farko da ya fara raba wa jama’a kayan azumi a duk fadin jahar.

See also  GWAMNATIN TARAYYA TA BAYAR DA HUTUN BIKIN MAULUDI

Rabon Wanda a ka yi shi ranar asabar data gabata ya bada buhunan gero 1500 shinkafa buhu 500 sukari buhu 500, sai kuma wasu kayan sana’a da ya rabar wadanda sun hada da Babura 55 kekunan dinki 110. Injin ban ruwan noman rani dana kayan lambu 550 injin walda 50.

Sanatan ya bayyana cewa, ayyukansa ba za su tsaya ba , don haka ma ya bude gidauniya wadda zata ci gaba da gudanar da ayyukan Alherin da yake yi. Bikin na bada kayan na azumi, ya samu halartar gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari CFR da shugaban SMEDAN, Alhaji Dikko Radda da shugaban APC na shiyyar funtua. Alhaji Bala Abu Musawa da wasu kwamishinoni da dimbin jama’a wadanda suka nuna jin dadinsu da farin cikinsa da wannan aikin Alheri da yayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here