GUDUN HIJIRA A BIRNIN KANO

0
585

GUDUN HIJIRA A BIRNIN KANO

Daga Danjuma Katsina

Tun bayan fitowar littafin OUT OF THE SHADOWS na kayode fayemi gwamnan Ekiti, wanda har sunayenmu suka fito na zama na samu karfin gwaiwar fito da nawa mai suna GUDUN HIJIRA A BIRNIN KANO.

Kafin fito da shi ga jama’a, na tsara shafin adabi na Taskar labarai ya fara buga shi, da wasu hotuna na tarihi da muka dauka tun a wancan lokacin. Akwai darussa abin koyi

Daga yau har karshen azumi zan rika tsakuro Kadan, ina sanyawa a shafin Katsina City News 1$2 da kuma shafin Facebook.

A labaran za ku ji yadda mutum kan zama dan ko me ta tafasa ta kone. Da yadda aka dogara ga Allah sai ya kare ka da ababen al’ajabi.

Ga kadan daga littafin GUDUN HIJIRA A BIRNIN KANO, da fatan zai rika nishadantar daku a wannan wata mai alfarma.

*Jumma’a a birnin Katsina 1996 (1)*

Wata jumma’ a labari yazo cewa yan sandan kwantar da tarzoma sun aukama muzaharar tunawa da ranar kudus da ‘yan uwa musulmi ke yi duk shekara a birnin Zaria, bakin kofar Doka lamarin ya faru an kashe ‘yan uwa da yawa an kama wasu.

Da safiyar asabar aka ce tarin jami’an tsaro sun je gidan Malam Zakzaky, sun tafi da shi. Lahadi ‘yan sanda na bin gidaje ‘yan uwa dake Zaria suna ta kama su.

Ina a Katsina amma mata ta, da ‘ya’yana da kuma kanwata duk suna a Zaria. A gidan da gidan rediyon kasar Iran suka bani ( lokacin ina yiwa rediyon Iran aiki, ni ne wakilinsu tilo a kasar, ina kuma yiwa Al mizan) wanda gidan yake tsakiyar gidajen ‘yan boko da masu rike da manyan mukaman gwamnati.

Lahadi da yamma na nufi Zaria,tun daga tasha da aka sauke ni naga garin kamar anci garin da yaki. A gida na, na iske matata Rukayya Danladi Saulawa da dana Muhammad da diyata Hadiza ( bani na haifeta ba, amma ni na rike ta) da kanwata Aisha duk lafiyarsu kalau da yaron gidana Mustafa. Mata ta yi ta bayyana mani abin dake faruwa.

Da safiyar litinin aka yi wata gagarumar jerin gwano a Kaduna wanda har soja suka fito da tankokin yaki da jiragen yaki masu tashin angulu, gwamnan lokacin kanar Hamid Ali ya yi jawabi mai tsauri ga jihar, daga nan sai kame kame suka kara tsauri.

Na yanke shawarar iyalin gidana baki daya su koma Katsina, muka tsara yadda aka kaisu tasha suka tafi, sun tafi da kwana daya jami’an tsaro suka mamaye gidana ina ciki amma nayi shiru kamar ba kowa. Allah ya taimake ni basu balle ba kwanansu biyu ana uku suka tafi ina ciki. Koda na tabbatar sun tafi na bude gidan,na baro shi,ban kara komawa ba da sunan zama .har yau.

SAI A KASHI NA BIYU kun ji ya ta kaya..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here