A WANI GARI
daga Taskar Labarai
A wani gari ne babba a kasar Hausa, wani mutum yayi zaman doya da mahaifinsa, har ana tsammanin mahaifin nasa ya tsine masa albarka.
A wani gari abokin sa ya rungumi wannan da ake zargin tsinuwa na bi ya mai da shi mutum. A wani gari abokin yaci amanar abokin nasa da ya rungumeshi a lokacin da hatta ubanshi ya gargade shi kan shi.
A wani gari wani duk da matsayi da kudin da ya ke sarrafawa a wani gari mahaifiyar wani ta bar duniya da bakin cikinsa a wani gari mahaifiyar wani tana nadamar haihuwarsa a wani gari tsohuwar tayi masa baki da sai ka zama annoba a cikin Al’umma.
Wani shugaban bai dauki amana komai ba a wani gari wani bai dau badala da mata wata tsiya ba.
A wani gari wani bai san darajar watan Ramadana ba a wani gari wani bai san me za a yi ko kar ayi a watan ba. A wani gari wani dakikin bai san cewa fitina kwance take ba, kuma Allah ya tsine wa mai tado ta. A wani gari wani bai san cewa tada fitina na da sauki ba, amma kwanciyar ta sai da taimakon Allah.
A wani gari suna bukatar addu’ar al’umma don kuwa ga mai bakin uwa da uba yana neman jajibo masu ja’iba.
A kowane gari a kowace mu’amala in za ayi a tabbatar wanda za a yi dashi, ya rabu da mahaifansa lafiya.
A kowane gari da kowace mu’amala ku sani hakkin uwaye na tasiri a kan kowa.
Daga shafin Taskar labarai dake www.taskarlabarai.com da Facebook na jaridar taskar labarai da lambar waya ta whazzap 07043777779