Yadda Aka Samu Gawar Wani Babban Jami’in Soja a Dakinsa A Jaji

0

Yadda Aka Samu Gawar Wani Babban Jami’in Soja a Dakinsa A Jaji
Daga shafi zuma times hausa
A ranar 12 ga watan Mayun da muke ciki ne (Shekaranjiya) aka samu gawan wani babban jami’in sojin Sama da ya kai matsayin Laftanar Comando mai suna Solomon Franklin Derokoma a dakinsa da ke Barikin Horon Sojoji na kasa da ke Jaji, Kaduna.

Jami’in an samesa ne a mace kuma dakin a kulle, a washe garin da za su tafi kasar waje domin yin kwas da abokanan aikinsa.

Solomon, shi ne mukaddashin Komandan rundunar jami’an da za su tafi karo karatu, sai dai kowa ya shirya za su tashi amma ba a gansa ba a matsayinsa na wanda zai jagoranci tafiyar. Nan take sai aka wuce zuwa dakinsa domin bincikoshi amma an tarar da dakin a kulle da kwado a ta waje, hakan na nufin ba ya nan.

Hakan bai gamsar da wadan da suke je dubiahi din ba, dan haka sai suka fasa kwadon domin leka dakin, nan kuwa aka samu gawarsa a kwance tare da rafkeken dutse a gefensa kuma hakan na nuni da cewa kasheshi aka yi har gawar ta fara kumbura da wari.

Shi da marigayin dan birnin Fatakwal ne daga jihar Rivers, kuma kwararre ne a fannin sarrafa bindigogi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here