AN BA SARKIN KANO KWAIRI…?
Daga Taskar labarai
Jaridar Taskar labarai ta gano cewa gwamnatin jihar Kano a satin da ya wuce ta baiwa sarkin Kano Muhammadu Sanusi II takadar tuhumar neman bayani.
Majiya mai karfi ta shaida ma Taskar labarai, an gabatar da takardar ana neman sarkin yayi wasu bayanai, me yasa da zai yi tafiya, bai fada ba, sai kwana uku kafin tafiyarsa?
Kuma da ya dawo me ya danya ya bari jama’a suka yi masa tarya ta alfarma? Har aka tara jama’a masu yawan gaske?
a kan waccar takardar ta tuhumar neman bayani, mun tuntubi mai magana da yawun gwamnatin, Kano Abba Anwar wanda ya shaidawa Taskar labarai cewa, bai san da maganar ba, Kuma bai ji ta ba.
Sarkin na fama da tursasawa da matsi daga gwamnatin jiha wadda ta dauka baya tare da ita. Hatta nasarar da wasu yan majalisun PDP suka samu a kotu, na a tsaida masarautun har sai ta gama sauraren shara’ar dake gabanta, ya batawa gwamnatin ta Kano rai.
Wata majiya tace, yanzu za a fara rike kudaden da ake baiwa masarautar daga ma’aikatar kananan hukumomin jihar wai har sai an kammala shara’ar.
Majiyar tamu tace, dama an tsara daga wannan watan masarautar Kano zata rika amsar kudaden kananan hukumomi takwas ne kawai.
Yanzu da hukuncin kotu ya bayyana za a rike suhar sai sun daga kara ko an gama waccar shara’ar. Majiyarmu tace yanzu fadar gwamnatin ta Kano za ta sanyawa masarautar takunkumin tattalin arziki na sai baba ta gani, zargin da Abba Anwar kakakin gwamnatin ya karyata.
iIda yace gwamnatin bata rike da sarki a kan wata mummunar niyya. Majiyarmu ta tabbatar mana cewa, gwamnan na Kano ya rude a kan halin da ya shiga na karin masarautun da ya kawo cece kuce ya zamar masa gaba kura baya siyaki, a kan haka ya ruga Abuja neman shawarwari.
Taskar labarai ta gano cewa duk wannan yanayi da ake ciki sarkin na Kano bai yi zance halin da ake ciki da kowa baya yi shiru da sanyawa Sarautar Allah ido.
Tun da aka fara wannan badakala fadar ta sarkin Kano ke ta samun tausayawa da goyon baya daga ciki da wajen Najeriya.
Wasu kuma na tambaya ina Dattawan Kano ne?
…………………………………………………………………………
Taskar labarai jaridar da ake bugawa bisa yanar gizo tana a www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta na yanar gizo da lambar whatsapp ta 07043777779.