YADDA MAHARA SUKA MAIDA KATSINA MACUWARE
Daga Lawal Iliyasu Garba
Matsalar tsaro a kananan hukumomin Batsari da Safana dake jihar Katsina yakai matakin sai dai ace Inalillahi wa’ina ilaihi raji’un saboda a kowace rana sai kaji barayin shanu da masu garkuwa da mutane sun kai hari a wani gari ko dai su kashe rayuka ko kuma su kwashe dukiya ko kona gari.
Bayan harin da barayin shanu suka kai a Wagini daren ranar asabar 12/5/2019, da karfe 2:00pm na yamma barayin sunyi wa wasu matafiya kwanton bauna a hanyar Batsari ziwa Safana inda suka kashe mutum daya suka yi awon gaba da mutane 12 dukkansu ‘yan kasuwane da suka fito daga Anchau ta jihar Kaduna zuwa kasuwar Jibiya ta jahar Katsina.
Adai ranar ta lahadi da misalin karfe 6:00pm na yamma barayin sun mamaye kauyen garin Labo da Inwala dake cikin karamar hukumar Batsari inda su kayi awon gaba da duk dabbobin garin amma dai babu asarar rai.
A washe garin ranar Litinin kuma barayin sun shiga garin Hwahwara dake cikin jihar Zamfara su ka yi awon gaba da dabbobin garin, washe garin daren talata kuma maharan sun kai samamene a garin Baure dake cikin karamar hukumar Safana da misalin karfe 2:00Am na dare inda suka kashe mutum 4 sukayi awon gaba da wasu gami da duk dabbobin garin.
Tambayar da mutane ke yi kuwa ita ce, wai mike amfanin jami’an tsaron da aka jibge na sojo a yankin? duba da irin yanda ‘yan bindigar ke cin karensu ba babbaka a yankin.
Lawal liliya @ jaridar taskar labarai.