A DAKATAR DA SHUGABANNIN PDP NA KATSINA KUMA A BINCIKE SU

0

A DAKATAR DA SHUGABANNIN PDP NA KATSINA KUMA A BINCIKE SU
~~~~Takardar korafi daga PDP

Daga Taskar Labarai

Wata takardar ta korafi da jaridar Taskar labarai ta samu wanda wani mai suna Gidado Mighty ya sanya ma hannu kuma aka rabawa duk shugabanni PDP na kasa da kuma jihar Katsina.

Takardar an kuma baiwa hukumomin tsaro na kasa, tayi kiran da ya kamata a dakatar da shugabannin jam’iyyar PDP na Katsina a kuma bincike su.

Takardar wadda Malam Gidado Mighty yace suna wakiltar wata kungiyar ce, mai suna ‘yan PDP da basu kai shekaru arba’in ( KATSINA STATE PDP UNDER 40).

Bayan sun baiwa duk wanda ya cancanta a ofis na PDP na kasa dake Abuja da kuma wasu masu fada aji na PDP a Katsina da jami’an tsaro.

Sun kuma Raba ta ga wasu kafofin watsa labarai na kasar nan ciki har da Jaridar Taskar labarai.

Bincike da taskar labarai tayi ta gano takardar korafin ta shiga hannun duk wanda aka tsara a ofishin PDP na kasa da na Katsina.

Takardar korafin mai shafuka Goma sha biyu, ta fara ne da gabatarwa inda masu koken su ka ce sun rubuta ne a madadin mafi rinjayen ‘yan PDP dake Katsina. Kuma sun yi ta ne bisa kishi da maunar farfado da jam’iyyar ta PDP.

Takardar tayi korafin cewa, jam’iyyar ta koma da farko wasu mutane bakwai kadai ke juya ta, amma da zabe ya matso ta koma karkashin mutane hudu, su kuma suka rika tafiyar da ita kamar wata kungiyar asiri, takardar tace, aika-aikar wadannan ‘yan hudun suka kori mutane masu daraja da kima a jihar daga cikin jam’iyyar.

Inda takardar ta Jero sunayen wadansu daga cikinsu, su ka ce wannan ya jawo jam’iyyar ta yi asarar sama da kuri’u dubu dari biyar halak Malak.

Su ka ce ‘yan hudun nan masu tafiyar da jam’iyyar kamar kungiyar sirri sun fara yiwa jam’iyyar barna tun a zaben Deliget, wanda aka rika canza sunaye kamar canza hula, kuma da a ka je wajen taron fitar da dan takarar shugaban kasa, muna zargin sun amshi kudade hannun yan takarkari ba tare da Deliget na Katsina sun san me aka amsa ba.

Takardar korafin ta ce su wadannan ‘yan hudun muna zargin duk abin da aka zo da shi na kamfen sun rika rabawa a tsakanin su ne, misali motocin kamfen ba wanda zai ce ga yadda suka zo ga yadda aka rabasu.

Takardar korafin tace har yanzu ba wanda ya san nawa aka bada don zabe daga ofishin Atiku da kuma uwar jam’iyya, amma akwai maganganu masu yawo a kan kudaden
Abin da takaici, duk yan hudun nan ba wanda ya kawo karamar hukumar sa.

In ban da shugaban jam’iyya kuma dan takarar mataimakin gwamna Majigiri ba wanda ya kawo mazabarsa.

Takardar taci gaba da cewa, daga abin da muka kawo a sama shugaban jam’iyya na kasa ya kasan ce da tafka aika-aika a zaben da ya gabata da tafiyar da PDP a Katsina.

A kan haka muke rokon uwar jam’iyyar ta yi mana bayanin nawa aka baiwa jahar Katsina tun da daga zuwa fitar da an takara a Fatakwal har zuwa zabubbukan da a kayi?

Muna kuma rokon cewa daga abin da muka kawo a baya uwar jam’iyya ta kasa ta kafa wani kwamiti mai karfi, ta binciki aika aikar da su ka yi ma PDP zagon kasa wadanda wadannan mutane sune sila.

Mutanen kuwa sune Ibrahim Shema da Yakubu Lado da Salisu Majigiri da Umar Tsauri. Wadanda sune ‘yan hudu kuma matsalar PDP a Katsina.

Kwamitin ya binciki irin kudaden da suka amsa in ta kama a shigo da EFCC cikin maganar ayi don tsarkake jam’iyyar da kuma yi wa ‘ya’yanta adalci.

A dakatar da shugaban jam’iyyar da kuma sakataren ta na kasa Umar Tsauri a dakatar da tsohon gwamna Shema da dakatar da duk wata hudda ta jam’iyya da wadannan da muka kawo sunayen su a sama har sai an gama binciken da muke roko ayi.

Takardar an gabatar da ita ga shugaban jam’iyya na kasa wanda Taskar Labarai ta tabbatar da cewa ya samu kwafinsa, yanzu kuma tana ta yawo a hannun manyan ‘yan PDP.

Taskar labarai tayi kokarin jin ta bakin shugaban jam’iyyar Alhaji Salisu Majigiri abin yaci tura koyaushe wayoyinsa a kashe mun aika masa sakon wayar hannu shima ba amsa.


…………………………………………………………………………
Jaridar taskar labarai na bisa shafin www.taskarlabarai.com da sauran shafukan yanar gizo na Facebook, Instagram da YouTube da whatsap 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here