YADDA ‘YAN BINDIGA SUKE CIN KARENSU BA BABBAKA A BATSARI
Da misalin 6:40pm na ranar asabar 18/05/2019 wani
gungun ‘yan bindiga dauke da miyagun makamai akan babaura kimanin 150 suka yiwa kauyen Sabon garin Dumburawa dake karamar hukumar Batsari kawanya.
Inda suka yi ta harbi ba kakkautawa tare da tattara dabbobin garin, mun yi tozali da wasu ‘yan kauyen Dangeza su biyu da barayin suka harba sakamakon dauki da su ka yi yunkurin kaiwa, da yake kauyukan nasu suna kusa da juna.
Daga nan kuma sai aka ji wani bangare na yan ta’adar sun bulla ‘Yar laraba wani kauye dake yammacin Ruma inda suka kashe wani dattijo mai suna Salisu Teacher kuma su ka yi awon gaba da dabbobin garin.
Sai kuma suka tsallaka Salihawar Yarlarba inda canma su ka yi awon gaba da dabbobin kauyen (shanu), sai kuma sabon garin Wagini wani kauye dake nisan 1km da kudancin wagini inda su ka yi ta harbe-harbe.
Daga nan sai kuma suka tsallaka kauyen Dakya camma dai zancen duk daya ne da sauran kauyukan da suka je.
Wannan lamari yasa mata da yaran kauyukan da aka je masu suka fantsamo cikin garin Batsari gwanin ban tausayi, duk da an sanar da jami’an tsaro ‘yansanda da sojoji kuma mu tabbatar da ganin motoci takwas nasu amma dai duk kauyen da muka kira muji ko jami’an tsaro sun kai masu dauki sai su shaida mana cewa su basuji duriyar ko dan banga ba.