FADAR SARKIN KANO GA HAKIMAN KANO

0

FADAR SARKIN KANO GA HAKIMAN KANO

Daga taskar labarai

Masarautar sarkin Kano ta aika wata wasika ga dukkanin hakiman jihar baki dayansu. A wasikar suna shaida masu cewa su sani, har yanzu masarauta daya ce a birnin Kano. ita ce wadda sarkin Kano ke sarkin ta.

A wasikar wadda Taskar labarai ta samu kwafi tana fadawa hakiman su sani cewa, sun yi mubayi’a daya ce kuma bisa Kur’ani da Hadisi, mubayi’ar sun kuma yi ta ga sarkin Kano ne.

Takardar ta ce, ta tabbata akwai wata magana ta karin masarautu wadda maganar tana kotu, kuma ya kamata kowa yabi umurnin kotu, kamar yadda kotu tace a tsaya yadda ake ada.

Masarautar ta ce, kowane hakimi ya sani, umurni ko hani zai rika amsar shi ne, daga wajen sarki kwara daya na kano.

See also  YADDA SARKIN KANO SANUSI 11 YA GIRBI ALHERIN DA YA SHUKA A NASARAWA.

Takardar ta ce, duk hakimin da aka so a tilasta masa, ko ayi masa wani abu na wuce ka’ida, kar ya sabama dokayabi doka akwai lauyoyin da aka ajiye musamman wadanda za su tsaya mashi.

Takardar ta umurci kowane hakimi ya kara dagewa waken yiwa jihar da kasa addu’a.

Fitowar wannan wasikar ta gano yadda sarkin Kano ke da zuciyar zaki akan halin da gwamnatin jihar Kano ta saka shi.

Duk da yanayi da halin da ake ciki zuciyara a dake take ba abin da ya girgiza ta.

Don gani wasikar jeka shafin taskar labarai na Facebook, mai suna jaridar Taskar Labarai,.Ko shafinsa na yanar gizo dake www.taskarlabarai.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here