HABA ‘YAN MAJALISUN KATSINA

0

HABA ‘YAN MAJALISUN KATSINA

Sharhin jaridar Taskar Labarai

A jiya ne aka rantsar da gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari CFR a karo na biyu. Rantsuwar an yi ta cikin armashi da burgewa, kuma gwamnan yayi jawabi mai sosa zuciya.

Wani abun sha’awa shi ne yadda gwamnatin ta dakatar da duk wani shagali don tausayi da jajantawa ga abin da ke faruwa na hare-haren yan ta’adda a jihar.

Babban abin haushi da takaici da Allah wadai wanda ya faru a filin rantsuwar shi ne.

Bayan kammala rantsuwar gwamnan yana jawabin sa a tsaye, duk manyan baki suna a zaune suna saurare cikin girmamawa. Daga cikin manyan bakin nan akwai masu Martaba sarakunan Katsina da Daura da uwaye da Dattawan jiha da na kasa baki daya.

Ba wani dalili sai kawai aka ga ‘yan majalisar dokokin jihar sun bar mazauninsu, sun koma cikin motar da ta kawo su sun hakimce suka daga gilashin motar suka tada motar suka kunna esi.

Suka kuma sanya ‘yansanda suka yiwa motar kawanya kar wanda ya matso kusa da ita. Nan ciki su ka yi zamansu, har lokacin da aka gama sannan suka ce direba ya tuka motar suka bar filin taron.

Wannan dame ya yi kama? Me ya sanya haka? Sun fi karfin zama rumfar taro ne? Inda sarakuna da tsaffin gwamnoni ke zaune?

Tun a filin taron wannan aika-aika nasu ya zama abin magana da duk filin ana ta zundensu da nunawa.

Wannan ba alama bace ke nunawa cewa al’ummar Katsina ta zabo tumun dare? A wannan karon a majalisar dokokin jihar?

Ya kamata ‘yan majalisar su fito suyi wa jama’ar Katsina bayanin me yasa sukayi, waccan Saba ka’idar da girmama manya da na gaba? Wanda yake kama da rashin da’a. Manya na a kujera, ku kuna cikin mota? Yin bayani na da dadi ko kuma wannan abin Allah wa dai zai ci gaba da binku har abada.

Wannan shine ra’ayin Jaridar Taskar labarai.
…………………………………………………………………………
Taskar labarai jarida ce mai zaman kanta dake da cikakkiyar rijista tana kuma bisa shafin yanar gizo na www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta na Facebook, Twitter YouTube da whatsapp.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here