HON SALISU HAMZA RIMAYE DAN MAJALISSAR DA YA FI SANATA AMFAN.

0
754

HON SALISU HAMZA RIMAYE DAN MAJALISSAR DA YA FI SANATA AMFAN.

 

~~~ Gidauniyar Maigemu ta Raba Dinkin Sallah da Abinci ga Marayu da Masu Karamin Karfi 1000 a Karamar Hukumar Kankiya ranar 1/6/2019

Karamar hukumar Kankiya karamar hukuma ce da ke da dinbin tarihi a siyasar jihar Katsina. karamar hukuma ce da ta yaye zakararrun ‘yan siyasa da ake damawa da su a wannan jihar, wadanda suka hada da fitaccen dan siyasar na Isah Kaita da Arct Ahmad Dangiwa da Ahmad Baba Kaita da Kabir Baba Kaita da Habibu Gachi da Bishir Babba Kaita da Alhaji Saminu Kankiya da sauran ‘yan siyasar da suka yi zarafi a jihar Katsina

Sanin kowa ne cewa ana yin siyasa ne ko mulkin Damakuradiyya domin a kyautatawa al’umma kuma yi masu ayyikan da suke bukata wadanda suka shafi cigaban su ko kuma cigaban garuruwansu tare da tausaya masu a lokacin bukatar hakan.

Tun bayan dawowar mulkin farar Hula a shekarar 1999 karamar hukumar Kankiya take ta watangarya da walankeduwa wajen rashin dacen jagorori da zasu kyautatawa al’ummar domin su kwankwadi madarar damakuradiyya kamar sauran takwarorinsu da ke amfanuwa da wannan dama.

An samu mutane da su ka rike kujeru da dama a karamar hukumar Kankiya tun bayan dawowar Damakuradiyya wadanda suka hada da, Dan Majalissar Tarayya da Sanata da kuma kujerar Majalissar Jiha wadda Hon. Salisu Hamza Rimaye ke rike da ita.

Kaf din wadannan kujerun girama ne kawai da farfagandar iska, amma a zahiri babu wata kujera da ta kai wadda Salisu Hamza Rimaye (Maigemu) ke rike da ita amfani.

A tarihin karamar hukumar Kankiya kaf tun daga zamani Shehu Usman Danfodiyo har zuwa mamayar Turawa ba a taba samun wani dan siyasa ko kuma mai arziki da ya kamanta irin aikin da Salisu Hamza Rimaye ke yi ba domin taimakon al’umma da kuma kyautatawa talakawansa.

Tun bayan darewarsa bisa wakilcin karamar hukumar Kankiya ya kasance kullum babban gurinsa ya amfanar da mutanen yankin daga ayyukan da ake yi masu. Tarihi ya nuna cewa shi ne kadai dan majalissar da bai taba karakatar da wani aikin mazabarsa ba domin amfanuwar kansa da kudin (wannan kalubale ne ga kafutanin Yanmajalissun dokokin jihar Katsina).

A wannan zango da yanayin karancin kudi da ake ciki cibiyar sa ta Maigemu ta gudanar da taron da ba a taba yin sa ba a karamar hukumar Kankiya domin tallafa wa al’umma.

An bayar da dinkunan salla ga Marayu sama da dubu daya, domin suma su shigo gari daidai da dan kowa. Haka kuma an bayar da buhunnan Masara sama da dari da kudaden cefane ga masu karamin karfi domin su samu su yi abincin salla kamar yadda kowa zai yi.

A jawabin shugaban taron tsohon Gwamnan Mulkin soja na jihar Borno Kanal Abdulmumini Aminu mai ritaya ya yi kira ga dukkan jama’a da suyi koyi da wannan aikin aikhairin da Hon. Salisu Hamza Rimaye ke gudanarwa, ya kuma jawo hankalin marayun cewa idan suka dage suka yi karatu, kuma su ka yi aiki tukuru suma wata rana suna iya zama kamar Maigemu.

Shima uban gayya Hon Salisu Hamza Rimaye ya jaddada godiyar sa ga Allah madaukakin Sarki da ya bashi damar gudanar da irin wadannan ayyuka, ya kara da cewa wannan aikin an dade ana yin sa, amma dai ba’a fara bayyana shi duniya ta sani ba sai daga bara.

Taron ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen karamar Hukumar Kankiya da suka hada da babban bako na musamman Rt.Hon. Tasiu Musa Maigari Kakakin majalisar Dokoki na jihar Katsina, da Hon. Isa Ali Bindawa dan majisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar Bindawa, Hon. Nasiru Yahaya Daura dan majisar dokokin mai wakiltar karamar hukumar Daura, kantmomin riko na kananan hukumomin Kankia da Kusada Hon. Musa Maikudi Kankiya da Hon. Sama Mati, da Sakataren ilimi na karamar hukumar Kankia Mal Junaidu Abdulaziz Rimaye, da Shugaban kwalejin koyar da dabarun kiwon lafiya ta jiha dake Kankiya Alh Tanimu Master, da Ma’ajin Jamiyyar APC na jihar Katsina Alh Yusuf Kankiya.

Sauran sun hada da Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Kankiya Alh Danjuma Mamman Rimaye, da mataimakin Shugaban ruko na karamar hukumar kankiya Hon. Ashiru Hamisu Usman Magam wanda ya wakilci babban mai kaddamarwa Arc. Ahmad Musa Dangiwa, da manyan malamai, da wakilan Hakiman kankiya da Rimaye.

Wannan abin a yaba da Maigemu ya yi kalubale ne ga masu rikke da mukaman siyasa a karamar hukumar Kankiya domin su yi koyi da shi su tallafi al’ummar su ba su tsaya farfaganda da neman suna ba. Su sani cewa a kwai danginsu Marayu dake bukatar taimako, gida bai koshi ba, ba a tafi dawa ba.

Wannan rubutu kalubale ne ga ‘yan siysar Kankiya baki dayansu idan akwai wanda ya kama kafar Maigemu to ayyukansa su fito da shi ba farfaganda da neman suna ba. Ya na da kyau al’ummar Kankiya ku sani yi wa irin su Maigemu kutunguila a siyasa kamar yadda aka so yi masa duk da irin girmamawa da biyaya da yake wa masu farfaganda da neman suna abu ne da ya kamata ku fito ku yi yaki da shi. Kun dai ga irin alherinsa da kuma amfanin sa ga al’umarku.

Abdulrahaman Aliyu
Marubuci na Musamman da ke aiki da Jaridar Taskar Labarai
08119315573

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here