TSUGUNNE BATA KARE BA.
Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da Mai gari a kauyen Garin labo dake yankin karamar hukumar Batsari.
Maharan sun rutsa dashi 1:00pm a gonarsa dake can kauyen nasu watau garin labo daga bisani sukayi gaba dashi kan mashina kirar boko haram dauke da miyagun makamai sunata harbe harbe ba kakkautawa har suka shiga daji dashi batare da samun wata tirjiya ba.
Amman majiyarmu ta tabbatar mana da zuwan jamian tsaron soja jim kadan bayan maharan sun kammala nasu aikin.