“DAGA KATSINA STATE GOVERNMENT LODGE ABUJA FCT”

0

“DAGA KATSINA STATE GOVERNMENT LODGE ABUJA FCT”

Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Dr. Aminu Bello Masari CFR, (Dallatun Katsina/ Matawallen Hausa) ya karbi bakuncin Dr. Jelani Aliyu Shahararren mai kera motocin nan dan jihar Sokoto Shugaban hukumar kere-keren motoci ta kasa (NADDC), wanda kasar Amurika ta rike saboda hazakarsa wajen zana mota. Alh Faisal Jafar Rafindadi shine ya jagoranci tawagar ta Dr. Jelani Aliyu a Katsina State Government Lodge dake Abuja.

Dr. Jelani Aliyu Sokoto ya bayyanama Gwamna Masari irin nasarorin daya samu a rayuwa, da kuma irin kalar motocin daya zana da hannunsa kuma ya kerasu. wanda hakan yasa Kasar Amurika ta rikeshi tsawon shekaru masu yawa. Daga bisani ya dawo gida Nigeria, Gwamnatin tarayya ta bashi hukumar kula da kere-kere (NADDC). Yace” yadawo gida domin kasarsa ta amfana da basirar da Allah yayimasa.

Makasudin ziyarar ya nemi gwamnatin jihar katsina ta gina wurin da za’a bude kamfanin hada motoci kirar Nigeria a katsina kalkashin hukumar (NADDC) da yake jagoranta. Hakkin hukumar NADDC ne ta sanya kayan kamfanin. Cikin kamfani akwai inda za’a rika koyar da matasan mu gyaran motoci musanman motocin mu kirar zamani, pentin mota daidai dana fitowar mota. Bude kamfanin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasan mu. Kuma gwamnati zata samu kudaden shiga.

A cikin Jawabin Gwamna Masari ya nuna jindadinsa ga ziyarar da Shugaban hukumar ta NADDC Dr. Jelani Aliyu ya kawo masa. ya kuma jinjina masa. Kuma ya amince da aje ayi wannan ma’aikata a jiharsa ta katsina domin cigaban da zata kawo ba kadan bane, musamman yanda al’umma zasu samu abinyi. yace” Gwamnati zatayi iya kokarinta ta wannan ma’aikata ta kammalu cikin dan ƙanƙanen lokaci da yarda Allah.

Report:
Abubakar Shafi’i Alolo
Katsina Apc Social Media Crew

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here