GANDUJE NA KARA TAKURA MA SARKIN KANO
Daga Jaridar Taskar Labarai
Wani bincike da jaridar Taskar Labarai tayi ta gano gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na kara takura wa masarautar Kano da sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ta hanyoyi daban-daban.
A watan da ya gabata da ya tashi raba masu kudaden albashi, da na gudanar da masarautun. Sabuwar masarautar Karaye na bukatar miliyan Goma sha biyar sai aka bata miliyan ashirin.
Sabuwar masarautar Rano na bukatar naira miliyan Goma sai aka bata ashirin. ita kuma sabuwar masarautar Gaya na bukatar miliyan sha shidda sai aka bata ashirin .haka ma sabuwar masarautar Bichi na bukatar miliyan sha biyar sai aka bata miliyan talatin da biyar.
Ita kuwa masarautar cikin birni ta Kano na bukatar miliyan talatin da takwas da doriya. Sai aka bata miliyan ashirin
Kudaden na Albashi ne, da sauran ayyukan gudanarwa. A masarautar Kano albashinta kawai ya kai miliyan talatin. Don haka, sai dai su rage albashin ko kuma su ba wasu su hana wasu ko su Nemo ciko.
Sauran masarautun kuwa zasu biya albashi har su sami ragi. Gwamnatin zata kara nunka kudin da ta ke kashewa watsa labarai da sadarwa ga abin da suka kira wayar da kan mutane akan matsayar da suka dauka akan sarkin da masarautar ta Kano.
Ana kashe kudi ruwan kudi duk maganar da ake ba bashi komai za ayi ana zube kudin ne. Duk wannan abin da ake ciki, masarautar bata ce, kala ba kuma ba wani abu da ta ke yi na maida bugu ko kariya akan abin da ake mata.
Maganar sulhu da fahimtar juna sai ta taho kamar zata kan kama, sai masu amfana da rikicin sai su kara maida hannun agogo baya.
A tsarin na ganduje yanzu ba maganar kora ko dakatar da sarkin, amma za a takura masa har sai yaji a jikinsa.ya ajiye ko yayi ta zama cikin kunci. Kamar yadda wata majiya ta tabbatarwa da jaridar taskar labarai.
………………………………………………………………,,,,,,,…..
Jaridar Taskar labarai. Jarida ce mai cikakkiyar rijista tana bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta na Facebook..YouTube, Instagram da sauran su.