Budaddiyar wasika zuwa ga mai girma gwamnan jihar Kano Ganduje
Daga Sa’adatu Baba Ahmad
Ranka ya dade Mai Kano, da na samu dama a lokacin da mai martaba yake gabatar da ni a wajenka to, lallai da na d’an gutsura kokena akan hakiman Kano wadanda aka karkasa a gundumomin da ka yi masarautu. Bayan Babanmu Malam Idris Bayero Hakimin Bichi da ya yi tashin dolen dole bisa maida sabon nadinka cikin gidan masarautarsa akwai hakimai da yawa da ake barazanar kora idan ba su bi masarautunsu ba, na ga wata takadda da aka rubutawa wani hakimi da cewa ko ya gabatar da kansa a wata masarauta da garinsa ya fada a cikin awa ashirin da hudu Ko kuwa a tsige shi.
To lallai shi wannan hakimi tun a farko ya karbi umarni amma bayan da ya je waccan masarauta ya gamu da wulakanci dole ya komo gaban sarkin Kano ya zab’i mutuncinsa fiye da mukaminsa. Baba raba hakiman nan da mukamansu da garuruwan da suka yi shekaru fa zai jawo maka matsaloli da yawa daga ciki akwai hasashen cire soyayyar jam’iyyar Apc daga zukatan al’umma daga ciki akwai yiwuwar rabuwar kai tsakanin magoya bayan tsohon hakimi da sabon hakimi sannan kai kanka zaka tara dubban makiya masu yawan gaske.
Kuma wani abu da nake hange shi ne Baba lokaci yayi da zaka sayi soyayyar mutane in ana siye da kudi ko kyautatawa domin da kyautatawa ake mallakar mutane ba da tirsasawa ba, kowa fa aka tab’a mukaminsa cewa zai yi lokacin Ganduje aka kwace min sarautata. Dukkan wadannan hakimai na Kano mutane ne masu ilimi da martaba sun rike manyan mukamai a kasar wasu tsoffin manyan ‘yansanda ne wasu ambasadodi wasu dararktoci da ‘permanent secretaries’ bayan sun yi ritaya suke dawowa gida a basu sarautu, hakan ya sa suke gudanar da sha’anin mulki bisa ilimi da jajircewa kaima wataran in shekaru suka ja za ka iya zama kamarsu kuma ba za ka so a yi maka irin haka ba.
Don haka Ina baka shawara Baba kar ka dubi shawarar ‘yan jagaliya wadanda suka maida haddasa husuma hanyar cin abincinsu ka dubi wannan matsala da gaggawa ka gyarata saboda in an yi shuka ba a san ranar da zata hudo ba. Kuma shi Allah yana kafa mulki inda adalci ko da kuwa da kafirci ne, kuma yana rushe mulki inda zalunci ko da kuwa da musulunci ne, kar ka bari ka zama silar wofintar da kokarin wadannan mutane masu martaba.
Nagode
Sa’adatu Baba Ahmad Daga Jami’ar Skyline da ke Kano a Najeriya.
Ina rokon ‘yan jagaliya don Allah kar ku tare wasikata a hanya ko ku yi neman abinci da ita.