DAN MAJALISAR DUTSINMA/KURFI YA BADA TALLAFIN MAGUNGUNAN CUTAR AMOSANIN BARGO( SIKLA) KYAUTA

0

DAN MAJALISAR DUTSINMA/KURFI YA BADA TALLAFIN MAGUNGUNAN CUTAR AMOSANIN bargo ( SIKLA) KYAUTA
daga jaridar taskar labarai
Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar kananan hukumomin Dutsinma da kurfi hon Armayau Abdulkadir ya bada kyautar magunguna ga masu cutar amosanin bargo( sikla) kyauta ga masu fama da lalurar har su dubu daya da tamanin da biyu 1082
Magunguna sun kumshi harda wadanda ke wahalar samu, kamar lemos,uptamin,achiprofen,proguanil.da sauran su
An bada wadannan magunguna ne, a asibitin Dutsinma a a jiya laraba 19 ga yuni wadda tayi dai dai da ranar masu wannan matsalar ta duniya.
Magungunan Wanda kudinsu na da yawan gaske za a Raba su ne ga wadanda sukayi rijista da asibitin kuma aka tabbatar suna fama da wannan ciwo.
Dan majalisar ya bada tallafin karkashin wata gidauniya mai suna gidauniyar aikata Alhairi..Wanda sakataren gidauniyar Malam ibrahim bature Dutsinma ya wakilan majalisar tarayyar .hon armayau abdulkadir
Masu cutar ta sikla zasu rika amsar magungunan a kyauta.daga inda sukayi rijistar sunayensu aka tabbatar da matsalar tasu
Mutane da yawa suka hallara wajen kaddamar da bayar da magungunan ciki har da babban likitan asibitin na Dutsinma wanda ya nuna jin dadinsa tare da JINJINA da godiya gashi da majalisar da kuma yi masa addu a da fatan Alheri.
Magungunan cutar sikla suna da tsada kuma suna da wahalar samu,kuma ana shan su ne akan kari..
Wadanda suna da wahalar yawan samu ga mai karamin karfi.wannan ya Sanya tallafawa daga masu mulki da masu hannu da shuni yake da muhammaci
Sikla wata cuta ce da tafi wahalar da masu da ita har zuwa sukai shekaru talatin wasu kuma takan nakasa su kafin su kai wadannan shekarun .
Amma shan magani akan Kari na rage radadinta , yana kuma rage,illarta a jikin mai ida. Ba a daukar sikla ana haihuwar masu ita ne,

Wannan taimakon da Hon Armayau ya bada Wanda kuma akace zai ci gaba abin a yaba masa ba ne.kuma ayi masa addu a.
Duk mutanen da jaridar nan ta gama wasu, wadanda suka amfana sun nuna jin dadinsu da wannan dauki da aka kawo masa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here