WASIKA GA GWAMNAN KANO AKAN MASARAUTAR KANO

0

WASIKA GA GWAMNAN KANO AKAN MASARAUTAR KANO.
Daga  Danjuma katsina.
Bayan  gaisuwa da girmamawa na rubuto  maka wannan wasika ne,  don  shaida maka tunanin al ummar  dake  wajen kano akan abin dake  faruwa a kano   tsakanin gwamnatinka da masarautar  kano.
Da  farko  ina son ka sani  kano  cibiya ce,ta  duk  wani  hausa/fulani  dake  duniya.cikin hausa/fulani goma na  duniya.biyar  nada alaka da kano  kota auratayya, jini,asali ko kasuwanci kowata  hudda mai karfi.
Duk  jihohin dake da makwabtaka  da kano suna da alaka ta kut da kut  da kano  ta daya daga abin da  fada a baya.misali a jaha ta katsina.yankin sanatan  funtua.mafi  yawansu asalinsu  kanawa ne.haka  yake  a yankin sanata  ta mazabar daura,hatta katsina ada  tana karkashin kano ne a zamanin  mulkin turawa.
A  katsina ta tsakiya,kusan  gida takwas  cikin  goma nada wata alaka da  kano,ta auratayya,jini,asali, ko kasuwanci ko wata  hudda mai karfi .ni    marubucin nan  tsatso ne daga jinin zuriyar  Malam muhammadu bakatsine,da yar uwarsa  malama jibado.wadanda katsinawa ne a asali amma dasu  akayi  jihadin  shehu usman dan fodio a kano.kuma  sun taka rawa  sosai kamar  yadda  tarihi  ya tabbatar.
wadannan dalilai  suka  sanya,duk  abin da ya  shafi kano  duk  duniyar  hausa/fulani kan amsa.kuma  yakan  zamar kamar  amo ko ina kaji ya dauka.akan shiga damuwa akan lamarin sosai.
Yallabai, kana  bani  tausayi, don ana misalta ka da mutumin kirki, mai hakuri wanda  miyagun mutane ke sarrafawa.don  haka wani  lokaci  sai ka dau matsayi bisa kuskure a lokacin da bai  dace ba.sai  ka zama baka da goyon baya .
Rabuwarka da kwankwaso,an  dauka kaine kayi  butulci.don kwankwso  ya kasance  tare da kai a  duk tsawon zamanku  shekaru  takwas yana rike da mukamai  baku da gwamnati a kano.
kayi  ta  daukar  matsaya na tafiyar da mulkin kano.wanda sukayi ta jawo maka karin bakin jini ga  duk  wani  mataki daka dauka, misali gina shaguna a filin idi,da ginin  gadar  kasa a hanyar  zariya.
Hoton bidiyon da ake  zargin kaine, inda wani mutum na saka dalar amurka a ljifun babbar  riga,da  hana binciken don tabbatar da  gaskiyar hotunan ya  sa alamar  tambaya  da yawa akan ka.
fara daukar  mataki akan masarautar  kano a cikin watan ramadan  wanda ya  dagawa duk  musulmin duniya hankali  ya kuma zama abin magana a wannan  wata mai alfarma.wannan ma  ya jawo maka bakin jini ba dan kadan ba.
A takaice yallabai,abin da gwamnatinka tayi akan masarauta a cikin azumi   ya  dagawa musulimi  duniya hankali a wannan wata mai alfarma.
Duk  wanda ke bin yadda lamurra ke  gudana na tsakanin gwamnatinka da  masarauta, yasan ba iklasi a ciki  sai dai wani aiki  don huce  takaici   wanda wasu ke zugawa ana yi.
Duk  kuma abin da ba Allah  bane asalinsa  baya  dorewa  ko  ba jima ko ba dade, babban abinda ya kamata mutum ya  fara kawowa a gabansa  ga duk abinda  za  fara  shine  Tarihin da zai  bari, wanda  kuma zai  rika binsa da farautarsa ko  bayan ransa.
Wace  nasara aka samu  da  matsayar  gwamnatin kano  ga masarauta? Rarraba kan Al umma daya mai karfin gaske,wadda  ke magana da murya daya ada.
kashe  dimbin kudade  don  gaisuwa da wayar da kan mutane akan matsayar da  gwamnati  ta dauka akan masarautar,wanda  duk  mai  bin shirye shiryen rediyo  da  sauran kafofin  sadarwa  yasan ana kashe kudaden  da  ya kamata a saka su  wani  wajen da ya dace.
kashe  kudade,don kawai  a  inganta  sabbi  masarautun, wadanda ya  kamata a saka su  wasu ayyukan gina Al  umma da yafi  dacewa.
Dauke  hankalin al ummar  kano  daga gaskiyar  abinda ke  ci   masu  tuwo a kwarya  zuwa tattauna abin da inda zai amfani  rayuwarsu  kai  tsaye.
Duk  a wannan ba inda  talaka  sai amfana,  sai  dai  ranar  hawa  na sallah   karama da Babba ayi  a inda  ya  fito  sai  kuma ranar  jumma aje  sallah da  kuma  zaman fada.
saboda  kowa  yasan cewa, a  mulkin  dimokaradiyya.kansila,ciyaman, dan majalisar jaha, na tarayya da sanata.sune  kai  tsaye  suke magana akan al ummarsu ba wani  sarki ko wata  sabuwar masarauta ba.
yallabai, wata rana zaka  bar  mulkin kuma bayan nan Allah  masanin wa zai amshe ka,kuma miye tsarinsa.A lokacin  duk  masu  zuga  ka zasu  guje maka.
wannan abin da ake   wata Rana kai zata  dawo maka da iyalinka.kai  ne  za ai  ta  kawo  tarihi ana danganta  shi  da  akai , a alokacin kowa zai  juya maka  baya  yana  fadin cewa  kai ne  ka  sanya  shi.
yana da  kyau   a  saka hangen nesa.  a kuma sanya kula   komai mutum zai  gabatar  ya  tuna cewa  wata  rana ya abin zai  dawo  masa  kuma  ya zama mai  tuhuma, mai bada  shaida   kuma alkalin kansa da kansa.
akan bincike na  masarauta, a  wannan zamanin da muke  a  ciki  wanene za a bincika  ya  tsallake ba a same shi  da laifi ba.?  wata  rana zaka bar  mulkin kana fatan  ayi  in maka binciken kwakwaf?
bincike,don bata  suna   bai hana abin da  Allah ya  tsara  bawa  zai yi  nasara  akan su na   Rayuwa.misali zamanin Abaca  na  shugaban kasa, ya sanya  anyi wa   tsohon gwamnan kano kabiru  gaya  binciken terere.wanda  aka rika  yada  abin a gidan rediyo  kai tsaye da  bada  labarin  sauran kafofin  watsa  labarai.yanzu  kabiru  gaya sanata ne,  daga  jahar kano a  karo  na uku.
ina rokon a  sa  hankali,lura  da  hangen  nesa.don gaba don wata  rana.ko don  zuriya  da iyali.da sauran al umma.
DANJUMA KATSINA.
Mawallafi ne  kuma  Dan Jarida.
ana iya  samunsa a: mdanjumakatsina@gmail.com
08035904408

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here