YADDA TAURIN KAI DA KIN DAUKAR SHAWARA YA JEFE SANATA TSOMOMUWA.
Daga Taskar Labarai
Labarin da yazo ma Taskar labarai shi ne lokacin da sanatan Adamawa yaci fuskar wannan yarinyar a shago, wani dan jarida da ya samu bidiyon, aai yayi niyyar shiga tsakani.
Don haka, yayi kokarin ganin sanatan Abba daga jihar Adamawa, amma sanatan yaki ganin shi, da kyar ta hanyar wani abokinsa suka hadu.
Dan jaridar ya nuna sanatan illar fitar bidiyon, sai sanatan yace sai me aje a dora shi komai ta tafasa ta kone.
Dan jaridar ya sake samun wani dan uwa ga sanatan yace ya nusar dashi illar fitar bidiyon. Don haka yaje ya samu yarinyar nan da ya buga ya bata hakuri, su dai dai ta.
Da yaje ya samu sanatan, sai yaki saurare su, yace shifa yanzu sanata ne wanda har shugaban kasa na iya bukata a wajensa don haka ba wanda ya isa yayi masa kome.
Dan uwan na sanata ya samu dan jaridar yace ya fitar da hannunsa,koda dan jaridar yaji haka sai yace to shikenan.
Dan jaridar sai ya ba gidan jaridar Premium Times. Bayan sun tabbatar da ingancinsa, sai suma suka fara neman sanatan don ya fadi nasa bangaren, amma sanatan yayi ta daga masu kai, yama ki saurarensu.
Da suka gama ajiye hujjojin yunkurin ganin sanatan da yaci tura sai suka sake shi a bisa shafinsu.Yanzu labarin ya zamarwa sanatan fitina a duniya.