PROF. MOHAMMED NASIR SAMBO SABON SHUGABAN HUKUMAR NHIS TA KASA.

0

PROF. MOHAMMED NASIR SAMBO SABON SHUGABAN HUKUMAR NHIS TA KASA.

PROFESSOR MOHAMMED NASIR SAMBO, MBBS, MIAD, FWACP, Cert (WBA).

An haifi Prof. Muhammad Nasir Sambo a Zaria ta Jihar Kaduna a cikin shekarar 1968

Shi kwarren likitane, wanda ya dade yana bautama kasarsa da al’ummar kasarsa, Sambo mutun ne da kwarewarsa ta kai kololuwa har duniya ta yadda dashi. Sambo na cikin sahun mutanen da suka kawo chanje-chanje a fannin lafiya.

Kafin samun ci gabansa shi ne shugaba mai kula da kwalejin koyan aikin litita ta jami’ar Jihar Kaduna KASU. Tsohon mataimakin Dean na tsangayar koyan aikin likita na jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria.

Tsohon mataimakin Darakta, kuma maikula da shiryar Arewa masu yamma, na hukumar kula da lafiya ta firamari health care.

Tsohon mataimakin Janar manaja mai shugabantan community Based social NHIS Abuja.

Mamba ministerial wanda suka hada hannu da wasu masu zaman kansu, suka fito da wani tsari na lafiya, har ila yau mamba na ministerial Technical Group wanda suka karfafa wani tsari maisuna National Health Srategic development plan.

Babba jami’i na musamman wanda suka tsara wata mahaja mai suna Blue print for Acclarating, PHC, wanda kuma aka kaddamar dashi a Nijeriya da taken NPHC A.

See also  WATA CIBIYA TA KARRAMA SHUGABAN JAMI'AR NOUN FARFESA ABDALLAH UBA ADAMU

Yana cikin wanda suka suka fidda wani jadawali Resouce Person Health Sector Reform Agenda.

Shi ne ya shugabanci wata hukuma ta lafiya wacce take karkashin (NCH), kuma jami’ne da ake tuntuba domin neman shawara ko karin bayani, ko neman mafita akan wani al’amari da ya shafi lafiya a hukumomin UNICEF, UNFPA, DFID, da British council.

Sambo na cikin masu shirya jawabawar kwalejin koyon aikin likita ta afrika ta yamma.

Ya taba zama shugaban quality Assurance a tsangayar kwalejin koyan aikin likita ta afirika ta yamma, mamba na Accreditation a kwalejin koyon aikin likita ta afirika ta yamma, mamba NUC panel of Excellence na jami’ar Benin, shugaban manyan masu sa Ido da kai ziyarar bazata na kwalejin koyan aikin jinya da Unguwar zoma ta kafanchan, ya na cikin manyan masu fada aji da zartarwa na asibitin Barau Dikko, malamine da yake koyarwa wacce bata din din din ba a jami’ar Aberdeen Scotland.

Muna tayashi murna Allah ya tayashi riko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here