ME YA HANA MAGAJIN GARIN DAURA GODE MA SARKIN DAURA. ?

0

ME YA HANA MAGAJIN GARIN DAURA GODE MA SARKIN DAURA. ?
Daga Taskar labarai
Magajin garin Daura, Wanda aka sace ya kwashe kwanaki wajen miyagun da suka dauke.Cikin taimakon Allah yan sanda suka kubutar dashi a satin da ya wuce.
Bayan kubutar dashi, ya wuce Abuja don zuwa asibiti duba lafiyarsa.hotunan sun nuna kubutar dashi da kuma zuwansa Abuja
A yau ya fitar da wani sako Wanda gidan talabijin na kasa NTA hausa ya watsa. Kuma sakon ke ta yawo a shafukan sada zumunta na yanar gizo.
A sakon ya jero duk wasu da suka taka rawa muhimmiya wajen ganin Allah ya fito dashi
Da yazo wajen sarakuna.sai ya fadi sarakunan katsina amma bai fadi sarkin daura ba.ya kuma gode da JINJINA ga mutanen daura amma bai fadi sarkin daura ba.
Wakilan taskar labarai sun kalli sakon da yawa..sun kuma buga waya don neman haske .ba Wanda ya San dalilin magajin garin daura yaki fadin sunan sarkin daura a godiyarsa sai Allah sai kuma shi magajin garin na daura.
Wani abin da taskar labarai suka lura dashi magajin garin daura yana .karanta jawabi ne.rubutacce .! Ana iya mantuwa babba na sunan sarkin daura a rubutattcen jawabin da aka .karanta Alloon talabijin ? Kuma aka gyara shi aka sake kalla kafin a sake shi ga duniya ta gani ?
Wannan shine nazarin da jaridar taskar labarai keyi
………………………………………………………………………..
Jaridar taskar labarai jaridar ce mai cikakkiyar rijista dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta na Facebook, Twitter you tube da Instagram..tana yar uwa da ake bugawa da turanci mai suna The links news .dake www.thelinksnews.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here