HAJJIN BANA: AN KADDAMAR DA TASHIN ALHAZAI A JIHAR KATSINA DA MAHAJJATA 477
Abdurrahaman Aliyu
@ journey to the holy haramain
Jirgin farko na na kamafanin Max Air samfarin, ya bar filin saukar jirage na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina dauke da rukunin farko na Alhazan jihar zuwa Jidda da misalin karfe 7:10 na yammacin ranar Laraba.
Jirgin wanda ya ke dauke da mutane 495 daga cikin su akwai mahajjata 475 sai kuma ma’aikata da jogorori guda 20. Daga cikin al’umomin da jirgin ya dauka akwai rukunin maza mutum 287 sai rukunin mata 208.
Wannan bikin fara tashin Alhazan dai ya samu halartar gwamnan jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masari wanda ya wakilci shugaban kasar Nijeriya, sai shugaban hukumar Alhazai ta kasa Abdullahi Muhammad Mukhtar, Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, shugaban rukunonin kamfanin Max Air Alhaji Dahiru Barau Mangal, shugaban majalissar dokoki na kasa wanda ya samu wakilcin Sanata Kabir Abdullahi Barkiya, Amirul Haji na Jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal da sauran su da dama.
Da yake jawabin maraba shugaban hukumar Alhazan ya yi wa mahajattan barka da zuwa da kuma fatan Allah ya kaisu lafiya ya maido su lafiya. Ya roke su da su zama wakilai na gari a kasa mai tsarki har zuwa lokacin da zasu dawo.
A madadin sarakunan jihar Katsina shima Sarkin Katsina ya yi kira ga alhazan da su zama masu bin doka da oda da kuma yi wa Nijeriya addu’a a lokacin da suke a kasa mai tsarki.
Gwamnan jihar Katsina kuma wakilin shugaban kasar Nijeriya ya kara jawo hankalin Alhazan da su zama wakilai na gari a kasa mai tsarki, kar su aikata wani abu da zai bata sunan Nijeriya a kasar Saudiyya.
Haka kuma ya kara yin kira garesu da su yi wa kasar su addu’a neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa, kasantuwar addu’ar Alhazai karbaba ce.