NUJ TA SHIGA TSAKANIN JARIDAR TASKAR LABARAI DA GIDAN REDIYON JAHAR KATSINA

0

NUJ TA SHIGA TSAKANIN JARIDAR TASKAR LABARAI DA GIDAN REDIYON JAHAR KATSINA

Daga Taskar Labarai

Kwamitin Dattawa na kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Katsina (NUJ) a yau sun zauna don tattauna matsalar da ta kunno kai tsakanin jaridar Taskar labarai da kuma gidan rediyon jihar.

Bayan doguwar tattaunawa an kafa kwamitin mai karfi karkashin shugaban gidan talabijin na kasa NTA da wasu Dattawan kungiyar domin su zauna da mawallafin jaridar Taskar labarai Muhammad Danjuma da kuma shugaban gidan rediyon Alhaji Sani Bala Kabomo, don gano ina ne aka samu matsala kuma a warware ta.

Kwamitin Dattawan zai zauna da wadannan shugabannin guda biyu a ranar Talata mai zuwa. A sakatariyar kungiyar ta NUJ dake tsohon ginin KTTV Katsina.

See also  BAYAN SULHU; SU WA SUKA KAI HARI A BATSARI?

Don haka editoci da marubutan jaridar sun jingine da dakatar da duk wani rubutu akan gidan rediyon Katsina. Saboda darratta zaman da za ayi ranar Talata mai zuwa wanda kwamitin Dattawan kungiyar ya kira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here