Hajjin Bana 2019 Katsina.

0

Hajjin Bana 2019 Katsina.

Abdulrahman Aliyu
@Jorney To The Holy Haramain

A Daren jiya Alhamis 11/7/2019 da misalin ƙarfe 2:01 jirgin Max Air ya sauka a filin saukar jirage na ƙasa da ƙasa na Umaru Musa Ƴar’adua dake Katsina. Domin yin sawu na biyu a cigaba da ɗaukar mahajjatan jahar Katsina.

Mahajjatan da suka fito daga wasu ƙananan hukomomin shiyyar , Funtua sun kwana a filin jirgin suna jiran isowarsa.

An gudanar da tantance Alhazan cikin tsari da kyakyawan yanayi. Jirgin ya ta shi daga filin saukar Jiragen kimanin karfe 5:00 da mintuka na asubar yau Juma’a tare da mahajjata 495 sai kuma Jami’an hukumar Alhazan da zasu taimakawa mahajjatan su 8. Ya zuwa hada wannan rahoton dai jirgin ya sauka a Filin saukar jirage na kasa da kasa da me Jidda a Saudi Arebiya Lafiya da mahajjatan.

See also  PDP ta gudanar da taron haɗin kai na ya'yan jam'iyyar a Katsina 

Ba a samu wani korafi ba ko koke kan yadda daga mahajjatan sai dai akasin bacewar Fasfot din wata Hajiya guda daya, wadda ake kyautata zaton ya fadi ne a cikin motocin da suka wo jigilarsu daga sansanin alhazai zuwa filing saukar Jirage na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina. Kama jami’an hukumar suna bakin kokarinsu domin gano matsalar da kwantar wa Hajiyar hankali

Muna fatan Allah ya sa a yi Hajji karbabbiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here