Na shafe shekara 2 a kurukukun Saudiyya duk da kotu ta wanke ni…

0

Na shafe shekara 2 a kurukukun Saudiyya duk da kotu ta wanke ni…

~Alaramma Ibrahim Ibrahim

Alaramma Ibrahim Ibrahim mahaddacin Alkur’ani Mai girma ne, dan darikar Tijjaniyya, dan failar Shehu Ibrahim Inyass RA ne, dan asalin Jihar Zamfara da hukumomin Saudiyya suka kama shi bisa zargin shiga kasar da haramtattun kwayoyi shekara biyu da rabi da suka wuce.

A hirarsa da Aminiya ta tarho daga ofishin Jakadancin Najeriya ya bayyana yaddda lamarin ya faru.

Hukumomin kasar Saudiyya sun tsare ka bisa zargin shiga da haramattun kwayoyi, yaya abin yake?

To wannan al’amarin ya faru kimanin shekara biyu da rabi da suka wuce. Kuma yadda abin ya faru shi ne, ni dai na zo nan Umara ce, ina cikin wadanda Gwamnatin Zamfara ta ba kujerar Umara a wancan lokaci. Mun tashi daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano da muka sauka a Jiddah, sai muka shiga motar zuwa Madina. Muna masaukinmu, har mun fara shirin barci misalin karfe 12, sai muka ji ana kwankwasa kofa. Mu uku ne a dakin da yake ba mu rufe dakin ba, sai muka ga wadansu mutane cikin farin kaya sun fado da karfin tsiya. Sai suka rike mu, suka danne ni a kan gado suka mayar da hannuwana baya, suka shiga binciken dakinmu. Suka gama binciken ba su ga komai ba. Daga nan sai suka sa mini ankwa a hannu da kafa. Suka tafi da ni, ban san abin da ke faruwa ba.

To daga nan ina suka kai ka?

Sun tafi da ni ofishin ’yan sanda a nan Madina na kwana biyu a nan. Sannan sai suka ce ai matsalata a Jiddah ya kamata a duba ta, muka tafi Jiddah duk ban san laifin da na yi ba. Har ma tambayarsu nake me na yi ne aka kama ni, suka ce mini su dai an ce musu su zo su tafi da ni ne kawai. Bayan mun isa Jiddah sai aka kai ni wajen mai gabatar da kara a madadin gwamnati suka fara yi mini tambayoyi. Suka dauko tafinta yana fassara min abin da suke cewa da Larabci. Nan ne suka fada min cewa ana zargina da shigo da wasu haramtattun kwayoyi.

Na ranste masu da Allah cewa ni ban aikata wannan laifi ba. Na tambaya ina aka samu kayan, bayan kuma ga shi an caje jakata ba a samu komai ba. Sai suka ce ba tare da ni suka samu ba, wai amma suna da wani bayani da ke nuna cewa na zo da kayan. Na kara rantse musu da Allah cewa ni ban sani ba.

To bayan sun gama yi maka tambayoyin me ya faru?

Washegari kawai suka tura ni kurukuku, bayan na yi kimanin wata biyu a kurukuku sai suka fito da ni suka sake yi mini tambayoyi. Suka tambayi jaka launi kaza da kaya iri kaza. Na sake fada musu cewa ba ni ne da ita ba, kuma ban san daga ina wannan jaka ta fito ba don ba tawa ba ce.

Sai suka ce yaya aka yi suka samu jakar da sunana, na ce musu ni ban san da ita ba. Sai suka ce za su yi wa jakar binciken kwakwaf, kuma idan suka gano zanen yatsun hannuna a jakar, za su hukunta ni. Na ce su duba kyamarorin tsaronsu ma idan sun ga hotuna a kusa da jakar da suke magana to su yi mini duk abin da suka ga dama.

Sun sallame ka bayan tambayoyin?

A’a, sun mai da ni kurukuku ne, sai da na sake shafe wata 14 a gidan kafin a fara shari’a. Da aka fara shari’a, bayan wata biyu kotun ta wanke ni amma abin mamaki s ina tsammanin za su sake ni, sai suka ce an daukaka kara zuwa wata kotu a Birnin Makka, daga nan sai suka sake mai da ni kurukuku.

Ita ma wannan kotun ta sake wanke ni daga dukkan zargi. Duk da cewa kotu ta sake wanke ni a karo na biyu amma ba su sake ni ba, sai suka sake mayar da ni gidan maza. A takaice dai na shafe shekara biyu a gidan yari. Bayan nan sai suka ce ofishin Jakadancin Najeriya ya zo ya karbi belina. Zuwa yanzu na shafe wata biyar a ofishin Jakadancin Najeriya.

Me suke nufi da mika ka Ofishin Jakadancin Najeriya?

Sun ce sun ba da belina, na fahimci suna son su kara yin wata shari’ar. To amma daya daga cikin alkalan da suka yi wadancan shari’a ya ce shi ya yi shari’ar farko kuma bai ga wani laifina ba.

Ana rade-radin wata mata ce ta sa haramtattun kayan da sunanka a filin jirgin Malam Aminu Kano, ko kana da labarin haka?

Wallahi ba ni da wani labarin wata mata, hasali ma jakar da suke magana a kai har yau ban gan ta ba.

An ce Gwamnan Zamfara, Bello Mutawalle ya ziyarci Saudiyya ya zanta da jami’an kasar da na ofishin Jakadancin Najeriya da kai kanka, wane sako ya zo da shi?

Lallai ya zo kuma ya yi magana da ni da jami’an Ofishin Jakadancin Najeriya. Kuma na fada masa duk abin da ya faru. Ina godiya gare shi kwarai. Ina kuma kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da dukkan hukumomin da abin ya shafa su sa baki don samun mafita. Ina son komawa cikin iyalina. Rabona da su yau shekara biyu da rabi ke nan.

Alaramma Ibrahim dan uwa ne dan Faira danhaka yan uwa muna rokon a tayashi da addu’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here