HAJJIN BANA: KATSINA 2019 JIRGI NA 3

0

HAJJIN BANA: KATSINA 2019

Abdulrahman Aliyu
@ Jorney To The Holy Haramain

Ya zuwa yanzu da jirgin uku na mahajjatan jihar Katsina ya tashi zuwa kasa mai tsarki. Amirul Hajji na jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal da Yammacin nan ya gana da masu ruwa da tsaki kan aikin hajjin domin fuba irin cigaba da kuma matsalolin da aka fuskanta.

A lokacin da yake yi wa mahalarta taron maraba Amirul hajin ya bayyaba cewa, makasudun taron shi ne duba irin nasarorin da aka samu da kuma hakin da ake ciki ya zuwa yanzu.

Ya kuja yi kira ga masu ruwa da tsakin da su bayyana duk wasu abubuwa da suka gani game da jirage ukun da suka tashi, domin in akwai wata matsala ayi gaggawar magance ta, kafon jirgi na hudi ya zo.

Sannan kuma ya yi godiya da yabawa duk wasu da ke da alhakin gudanar da wannan aiki saboda irin gudumiwar da suka bayar na ganin an yi aikin cikin nasara ba tare da wani kalubale ba.

See also  GARURUWAN DA SUKAYI MAGANIN BARAYIN SHANU

Bayan gama jawabin marabar an cigaba da gudanar da taron ne a bude ta hanyar ba kowa dama ya fadi irin abubuwan da yake gani game da yanayin yadda ake gudanar da jigilar alhazan zuwa kasa mai tsarki.

Ya zuwa hada wannan rahoton dai akwai alhazan jihar Katsina dubu daya da dari hudu da tisi’in(1490) da suka samu isa Madina. A cikin wannan kaso kuma alhazai dari hudu da tisi’in da biyar(495) sun isa Makka domin yin aikin Umara da kuma addu’o’i kafin hawan Arfa.

Yanzu dai mahajjatan na jiran jirgi na hudu ne wanda ake tsammanin zuwan sa bada jimawa ba, domin daukar sauran alhazan da suka fito daga shiyoyyin Dutsinma, Kankiya, Mani, Daura, Malumfashi, Funtuwa, da kuma alhazn shiyyar Katsina ta tsakiya.

Muna fatan ayi Hajji karbabbiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here