SANATAN APC NA SHIYYAR FUNTUA BELLO MANDIYA NA CIKIN RIKICI

0
946

SANATAN APC NA SHIYYAR FUNTUA BELLO MANDIYA NA CIKIN RIKICI

Daga Taskar Labarai

Wata kungiya mai rajin ganin an samu ingantacciyar gwamnati a Arewa (Arewa Good Governance Initiative) ta yi Allah wadai kan yadda aka ci mutuncin Damakuradiyya a jihar Katsina, kan yadda Sanata mai wakiltar Shiyya Funtua Bello Mandiya ya shiga takara har ya ci zabe alhali kuma yana aikin gwamnati.

Daraktan huda da jama’a da yada labarai na kungiyar Nura Wada shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da kungiyar ta shirya jiya a garin Kaduna.

Kamar yadda ya fada Sanata Bello Mandiya ya tsaya takara a karkashin Jam’iyyar APC kuma ya ci zabe.

Ya cike takardar sheda hukumar zabe ta kasa mai lamba CF001 wanda ya ke a shafi na 3 sakin layi na 1 inda Bello Mandiya ya rubuta cewa ya yi ritaya daga aikin gwamnati tun a shekarar 2001.

Duk bayan wadannan bayanan sai kuma bayanai suka tabbatar da cewa Sanata Bello Mandiya shi ne shugaban ma’aikatn gida gwamnatin jihar Katsina, wanda takardar shedar karbar albashin sa ta nuna har watan Fabarairun 2019 an biya shi kudin albashi.

“Mu masu rajin ganin an samu ingantaciyar gwamnati a Arewa bamu ji dadin abinda Sanata Bello Mandiya ya aikata ba na yin takara da kuma cin zabe duk yana aikin gwamnati tare da gwamnatin jihar Katsina, wanda wannam saba doka ne. Sannan kuma ya shigar da bayanan bogi wadanda suka sabawa sashe na 140 da kuma sashe na 364 na kundin dokoki da hukuncinsu, wanda yanzu haka wata kotun majistire da ke Funtua na tuhumar shi da haka.

Ya kara da cewa babban gurinsu ne suga ana tafiyar da damakuradiyya ciki ingantacen yanayi da kuma gaskiya da rikon amana. Sannan ya kara da cewa sun samu labarin shire-shiren da gwamatin jiha ke yi na dauke shari’a da canza mata wuri kamar yadda doka ta ba babban kwamishin nan shari’a yin haka. Amma sai dai abin da yake so su sani koda an dauke shari’ar to ba za a taba gujewa adalci ba, dole ne za a yi ta kuka gaskiya zata yi halinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here