Gwamna Aminu Bello Masari ya amshi goron gayya da rukunin kamfanonin SIMBA ya aiko mashi kuma yanzu haka ya isa Kasar Indiya

0

 

Gwamna Aminu Bello Masari ya amshi goron
gayya da rukunin kamfanonin SIMBA ya aiko mashi kuma yanzu haka ya isa Kasar Indiya.

Wannan kamfani na SIMBA an kafa shi sama da shekaru talatin da suka gabata kuma yana kan gaba akan harkoki da dama wanda suka hada da samar da motoci, injuna da kuma dubarun noma irin na zamani, samar da wutar lantarki ta amfani da hasken rana, motoci da babura na safara, kwamfuta da sauran su.

Wannan ziyara za ta ba Gwamna Masari damar ganewa idanun shi yadda wannan kamfani ke gabatar da ayyukan shi tare kuma da fahimtar hanyar da Jihar mu za ta amfana da ayyukan wannan kamfani domin kuwa zai ziyarci wuraren da wannan kamfani ke tafiyar da al’amurran shi musamman bangaren da ya shafi noman rani da na damina, da kuma aikin saka tufafi (textile).

Bayan wannan kuma, za a gabatar wa Gwamnan gamsassun jawabai akan duk sassan wannan kamfani daga bisani a sa hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna da kuma aiki tare tsakanin wannan kamfani na SIMBA da kuma Gwamnatin Jiha. Wannan yarjejeniya ita za taba al’umma, musamman manoma, damar cin gajiyar ayyukan wannan kamfani, domin za a sami habakar aikin gona tare da bunkasar tattalin arziki.

See also  BARAYIN DAJI SUN KAI HARI KAUYEN DAN GEZA

Alhaji Aminu Bello Masari zai kuma ziyarci Jami’ar
ALAKH PRAKASH GOYAL SHIMLA UNIVERSITY, wadda shuwagabannin ta za su karrama shi lambar yabo, kuma daga bisani asa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da aiki tare tsakanin wannan Jami’a da kuma Gwamnatin Jiha. Wannan yarjejeniya za ta ba daliban jihar mu samun gurabun karatu a wannan Jami’a.

Wannan Jami’a, tana kan gaba a cikin jerin jami’o’in kasa da kasa da sukafi kyau a wannan shiyya ta kasar, kuma tana gudanar da kwasa kwasai a bangarorin Kimiyya da Fasaha, Injiniya, taswirar gini (Architecture) da sauran su, tun daga matakin digirin farko har ya zuwa na ukku.

A cikin wadanda suka rufa wa Gwamnan baya akwai Babban Sakatare mai kula da Ilimi mai zurfi (Higher Education) Alhaji Rabi’u Abdu Rumah, sai Daraktan Mulki na gidan Gwamnati Alhaji Falalu Bawale, akwai kuma Alhaji Salisu Mamman wanda ya wakilci cibiyar ciniki da masana’antu (Chamber of Commerce) da kuma manyan mukarraban Gwamnati.
Taken labarin
GWAMNANA KATSINA A KASAR INDIYA
daga Abdulhadi bawa. Ssa social media

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here