HAJJIN BANA: KATSINA 2019~~~ Ana gab da Kammala Jigilar Alhazan Jihar Katsina

0

HAJJIN BANA: KATSINA 2019~~~ Ana gab da Kammala Jigilar Alhazan Jihar Katsina

Abdulrahman Aliyu
@Jorney To The Holy Haramain

A daren jiya ne Jirgi na hudu mai dauke maniyyata aikin Hajji bana daga jihar Katsina su kimanin dari biyar da ‘yan kai ya tashi da filin saukar Jirage na Umaru Musa Yar’adu dake Katsina zuwa birni Madina.

Jirgin wanda ya tashi da rukunin maniyyatan aikin Hajjin bana da suka fito daga shiyyar Katsina da wasu daga shiyyar Funtua ya tashi daga Filin jirgin sama na Malam Ummaru Musa Yar’adua dake nan Katsina da misalin karfe daya na dare ya sauka birnin Madina da misalin karfe biyar da rabi na safiyar yau litinin.

Kafin tashin jirgin dai Amirul Haji na jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal ya kasance a filin jirgin domin ganin yadda ake tantance Alhazan da kuma yi masu jawabi da karfafa masu guiwa na rokon yi wa jihar Katsina addu’a da ma kasa baki daya.

See also  Matar Da Ta Shekara 41 Tana Shan Ruwa Kadai

Haka ma shugaban kamfanin Matasa Media Links wadanda ke buga Jaridar Taskar Labarai da jaridar The Links News shi ma ya samu halartar filin jirgin da yammacin jiya domin duba yadda ake tantance alhazan da kuma yi masu fatan alheri.

Ya zuwa yanzu dai jirgi daya ya rage a kammala jigilar alhazan jihar Katsina, wanda shi ma ake kyautata zuwan sa nan bada dadewa ba.

Muna fatan ayi Hajji Karbabba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here