SIYASAR ALH DAHIRU MANGAL MAKARANTA CE:

0

SIYASAR ALH DAHIRU MANGAL MAKARANTA CE:
_____________________
Daga Mainasara Balarabe Ruma

Siyasa na nufin hikimar neman alfarma don amincewa da wani ra’ayi domin tafiya tare.

Dimokaradiyya kuma na nufin bada damar zabi tsakanin wasu don tafiyar da harkokin jama’a. A takaice mulki da yawun mafi rinjaye cikin tsarin mutunta ra’ayin marasa rinjaye.
Wannan dama ta siyasa da Dimokaradiyya ga wadanda jama’a suka aminta da su na wani kayyadadden lokaci na nufin bai wa masu rinjaye shiga gaba wajen mulki da yanke hukunci kan bukatun jama’a.

Bisa Al’ada iya siyasa na tattare da sauki ga duk dansiyasar da ya iya zuba jarin taimakon jama’a, da kulawa da matsalolin jama’a, da kuma cudanya da jama’a ba tare da nuna Girman kai ko kyama ko angaranci ba. Wannan tsari shi ne jigon siyasar Alh Dahiru Bara’u Mangal, kuma makarantar nazarinmu a yau.

Tasirin Dansiyasa na karfafa ne idan yana da jimirin zuba jarin taimakon jama’a tare da zumunci da su. A taikaice mutum mai yawan alheri ga jama’a tare da karfafa tattalin arzikinsu zai iya tasiri matuka duk lokacin da ya nemi Alfarma ta kuri’arsu.

MANGAL A MAHANGAR TATTALIN ARZIKI:

Tattalin Arziki ne ginshikin rayuwar Al’umma. Saboda irin gwagwarmayar da Alhaji Dahiru Mangal ya sha a matakai daban-daban na rayuwa wajen fafatikar neman na kan sa, ya sadu da mutane iri iri, don haka ya san ciwon ko wane rukuni na al’umma. Wannan ne ya ba shi damar taimakon marasa galihu da karawa masu karfin tattalin arziki karfi, don su ma su iya taimakawa wasu.

A jihohin Arewa maso yamma, musamman Katsina, Kano, Kaduna, da Abuja, Alhaji Dahiru na zaman jigo wajen samar da jari da matsugunnai na masu sana’o’i daban-daban.

Wannan ya ba shi damar zama sahun farko wajen gina rayuwar Al’umma. Wani Babban Jari na taimakon jama’a shine kafa kamfanonin da suka dauki ma’aikata masu yawan gaske wajen gine-gine, aikin hanyoyi, sayar da mai da kuma uwa uba, kamfanin Jjirgin Ssama na Max Air da yanzu babu kamarsa, musamman ga aikin Hajji.

Max Air ya samu ne sanadiyyar matsalar da Alhazzan Katsina suka samu a shekarar 2005, sadda suka kasa zuwa aikin Hajji. Sanadiyyar wannan abin takaici ne Alh Dahiru Mangal ya nuna zuciyar Katsinawa, ya kafa Max Air. Marigayi Matawallen Katsina kuma Tsohon Shugaban Kasa, Alh Umar Yaradua, da Gwamna Shema ne suka karfafa daukar Alhazai daga katsina.

Wasu kyawawan halayen boye na Alh Dahiru Mangal sun hada da yafe basuka ga masu karamin karfi da ciyar da marasa lafiya da kuma kara jarin marasa karfi.

MANGAL A MAHANGAR ZAMANTAKEWA:

Iya zama da jama’a da karfafa zumunci ne jigon mu’amallar Alh Dahiru Mangal da Jama’a. Irin wannan zumunci na Alh Dahiru Mangal bai tsaya ga danginsa na jini ba, a’a, ya isa har ga sauran jama’a a rukunnan Saraki, Malamai, Tajirai, Yan Kasuwa da Talakawa.

Wannan kusanci da Al’umma ya ba Alhaji Dahiru damar taimakon jama’a matuka da kuma shiga gaba wajen sasanta rikici tsakanin mutane idan bukatar hakan ta taso.

Wannan kusanci da Al’umma ya bada damar fada a ji ga Alh Dahiru Mangal. Damar fada a ji cikin Al’umma Babban Jari ne ga Dansiyasa. Wannan dalili ne da ya ba Alhaji Dahiru Mangal zama makaranta ga sauran ‘Yan siyasa.

ALHAJI DAHIRU BARA’U MANGAL A MAHANGAR SIYASA:

Siyasa rigar ‘yanci ce da ke bada damar zabi ga mai zabe ta fuskar ra’ayi. Alh Dahiru Mangal ya dade ana damawa da shi a Siyansance saboda karfin fada ajin sa da kuma karfin jarin da ya ke zubawa a hada-hadar Siyasa. Sai dai lakantar halayen jama’a a da hulda da Jagororin Siyasa a matakai daban daban ya ba shi jarin iya karatun Alkiblar Siyasa a Nigeria. Cikin hukuncin Allah an dade ana damawa da Alhaji Dahiru Mangal a Siyasance.

Irin gudmuwarsa ta siyasa har ta kan kai wasu kasashe a wajen Nigeria. A mafi yawan lokuta Alh Dahiru Mangal kan bada hanya mafita idan siyasa tai sarkakiya. Haka kuma a kan saka shi gaba wajen neman goyon bayan jama’a ga Gwamnati. Kuma saboda dadaddar dangantaka, jama’a kan yi na’am da shawararsa.

Wani abin ban sha’awa ga salon siyasar Alh Dahiru Mangal shi ne na tsarin siyasa ba da gaba ba. Bisa doron wannan hikima ne ‘Yan siyasa daga dukkan jam’iyyu ke girmama Alh Dahiru Mangal tare da basu gudumuwa da karfafa dangantaka da su.

ALH DAHIRU MANGAL A MAHANGAR ADDINI.

Kamar uadda Allah Subhahu Wa Ta’ala ya ce: “Dukkanmu masu kiwo ne kuma za’a tambayemu kan kiwon da aka bamu.

Mahangar farko a addinance ita ce ta Iyali. Alh Dahiru Mangal ya yi tsayin daka wajen ba ‘ya’yansa ilimin boko da na zamani don su zamo masu amfanar Al’ummarsu. Ba kamar yadda aka saba ganin yayan masu hannu da shuni, saraki ko manyan masu mulki na zamewa a’lumma alakakai a tarbiyyance ba.

Bayan ba yaransa ginshikin ilimin addini da tarbiyya, Alh Dahiru Mangal ya saka yaransa ilimi mai zurfi a kimiya da fasaha da sana’a. Wasunsu sun fito da digiri na 2 mai daraja ta daya (1st Class) , a Ingila bayan gogayya da Turawa da sauran daliban duniya.

Wannan gogewa da Jarunta ne ya basu damar zama daraktoci a kamfunnan mahaifinsu, babban dankasuwa Alh Dahiru Bara’u Mangal .

~~~Mainasara Balarabe Ruma. Marubuci ne dan asalin karamar hukumar Batsari Jihar Katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here