HAJJIN BANA: KATSINA 2019~~Amirul Hajji na Jihar Katsina ya Bayar da Hakuri kan Jinkirin Da aka samu na Rashin Tashin Jirgi na Biyar a Yau.
Abdulrahman Aliyu
@Jorney To The Holy Haramain
Amirul Hajj na jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal ya gana da maniyyatan wadanda aka riga aka kirawo a sansanin Alhazai na jihar Katsina domin tafiyarsu kasa mai tsarki.
Alhaji Muntari Lawal wanda ya bayyana masu gaskiyar abinda ya jaza jinkirin jigilar tasu har sai Allah ya kai mu gobe, ya yi kira gare su da su dauki hakuri kuma su zamo masu biyayya tare da bin doka da oda dan ganin an gama jigilar lami lafiya.
A nasa bangaren babban Daraktan Hukumar Alhaji Muhammadu Abu Rimi ya shaida wa maniyyatan cewa, idan Allah ya kaimu gobe ne da safe za’a fara basu kudaden guzurinsu da sauran takardun tafiyarsu.
Daya daga cikin wakilan kamfanin da ke jigilar alhazan na Max Alhaji Danbaba ya tabbatar wa maniyyatan cewa idan Allah ya kai mu jirgi zai zo domin jigilarsu zuwa kasa mai tsarki.
Ya bayyana cewa, makasudin jinkirin zuwan jirgin ya hada da rashin kyawon hanya da kuma jigilar Alhazan jihar Taraba da Bauchi da za a yi jigilar su duk a yau din nan.