An Gano Harsashi A Cikin Kwakwalwar Shaikh Ibraheem Zakzaky

0

An Gano Harsashi A Cikin Kwakwalwar Shaikh Ibraheem Zakzaky

Daga Wakilinmu

Baya ga munanan ciwuka guda bakwai masu hadari da likitoci suka gano cewa Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky na dauke da su a jikinsa, a makon da ya gabata an kuma gano cewa akwai harsashi cikin kwakwalwarsa.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, a ranar Talatar da ta gabata, 23 ga watan July din 2019, yau kimanin kwanaki biyar, Shehin Malamin ya fuskanci matsanancin yanayi na rashin lafiya, wanda hakan yasa hukumomin da ke tsare da shi suka yi gaggawar daukarsa zuwa wani Asibiti a Kaduna a asirce da misalin karfe 5 na yammacin ranar.

Majiyar ta shaida mana cewa a nan ne kuma aka iya gano akwai wani kwanson harsashi a cikin kwakwalwar Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda yake fama da matsaloli da dama da suka hada da barazanar shanyewar barin jiki, tasirin guban dalma da ta Cadmium da kuma rashin idon bangaren dama da sauransu.

See also  Samar da ingantaccen Ilimi da aikin yi ga matasa ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a arewa

Majiyar tamu, har ila yau ta shaida mana cewa Shehin Malamin bai iya ko tafiya da kafarsa face a keken guragu da a kan tura mutum Saboda yadda jikinsa ya tsananta.

A ranar Alhamis 18/7/2019 ne dai aka sa ran kotu za ta bar Shehin Malamin ya fita Kasar waje don neman ingantaccen lafiya a wajen kwararrun likitoci, sai dai bukatar bata samu ba, a yayin da kotun ta dage sauraren bukatar fitan nasa zuwa asibitin waje zuwa Gobe Litini 29/7/2019.

Kuna iya ganin wasu daga hotunan Shaikh Ibraheem Zakzaky din a kan Keken na guragu, tare da hoton kan nasa da aka gano harsashin a jiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here