BATURE GAGARE BT (1958-2002.)

0

BATURE GAGARE BT (1958-2002.)
Cikakken sunanshi Ibrahim Lawal, an haife shi a cikin Lamama da ke Galadunchi a tsakiyar birnin Katsina. Yayi Gobarau Primary School daga 1966-1972. Barewa College Zaria 1973-1977. Yana daya daga cikin hazikai kuma masu matukar kokari da fahimta, ganewa da cin jarabawarshi a dukkan karatun da yayi.

Mahaifin Bature, Alhaji Lawal Gagare asalinshi mutumen Malumfashi ne aiki a Native Authority N.A ya kawo shi Katsina kuma ya rasu a lokacin Bature na da kimanin shekaru biyu da haihuwa a duniya.

Alhaji Tanimu Gagare Kafinta kuma mahaifi ga Kabir Tanimu Gagare shi ne ya rike Bature Gagare har ya girma.

Binta (Atutu) ita ce Mahaifiyar Bature Gagare mutunniyar sabon garin Eka da ke karamar hukumar Rimi ce. Mai kimanin shekaru 85 tana nan raye a Garin Kaduna.

Daga cikin sauran yan uwan Bature Gagare sun hada da Mariganya Binta, Marigaji Aminu, sai Mariganya Murja wadda ta rasu a ranar Jumaar da ta gabata 26/7/2019 kwana biyu bayan na yi hira da ita tare da wani Danuwanta Alhaji Ummaru inda na samu bayanai game da Marigayi BT.

Bature Gagare bai yi wani dogon karatun Boko ba duk da Kwakwalwa da Kokarin da Allah ya bashi. Amma ya fara Advanced Teachers College Kafanchan inda ya jagoranchi wata zanga zangar da ta yi sanadiyyar barin karatun na shi.

Ya dawo gida Katsina inda ya fara School of Nursing, nan ma aka samu wata matsalar makamanciyar ta ATC Kafanchan ya bar karatun.

BT yayi fice kwarai a harkar rubuce rubuce da tafiye tafiye. Littafinshi KARSHEN ALEWA KASA yayi fice sosai inda a 1980 ya zamo na ukku a kagaggun Labarai na Hausa da aka yi gasa a Kasar nan in ji Dr Garba Ashiwaju a mukaddimar littafin da ya rubuta kuma shi ne Daraktan Maaikatar Aladun gargajiya ta tarayya ya bayyana haka.

See also  LITTAFIN RAHOTON MARASA RINJAYE: YUSUF BALA USMAN DA SEGUN OSOB

Ya rubuta littafin TSULIYAR KOWA DA KASHI amma ba a samu damar wallafa shi ba sakamakon takaddama da aka yi da shi tun daga sunan littafin har ya zuwa bayanan da ke cikinshi.

Bature Gagare mutum ne wanda ya iya zane matuka kuma an ce duk abin da ya kalla za ya iya zana shi ba tare da kuskure ba balle bata lokaci.

Malamanshi a dukkan makarantun da yayi ya shiga ransu kwarai ganin irin kwazonshi da hazakarshi a karatu.

Ya rayu da mata ukku a lokutta daban daban da suka hada da Balaraba, Amina da Saadatu inda yana da Yaya shidda da suka hada da Kabir, Asmau, Amina (Junior) Aisha, Laila da Zainab.

Mutum ne mai matukar tsabta, son abinci na gargajiya kamar Danwake, Koko, Kosai, Kwado, Alkubus, Hura, Wake da Shinkafa.

Kadan daga cikin halayen BT sun hada da;
1. Son gaskiya da kamanta ta.
2. Mutum ne marar tsoro.
3. Abin shi ko abun duniya ba ya rufe mashi ido.
4. Yana da Sada zumunchi da son mutane.

Yana da abubuwan taajibi da ban mamaki kwarai da gaske.

Ya yi tafiye tafiye a ciki da wajen Nigeria da suka hada da Saudi Arabia, Algeria, Dubai da Malaysia.

Ya rasu a ranar 29/2/2002 a Lamama, Galadunchi sanadiyyar ciwon Lamoniya an kuma yi mashi sutura a Makabartar tsohuwar dantakun.

Kabir Umar Saulawa (P R O)
07034610481.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here