GADAR ZARE: Tare Da Dr. Auwal Anwar Yaudara: Daram! Dam!!

0

GADAR ZARE: Tare Da Dr. Auwal Anwar

Yaudara: Daram! Dam!!

Nijeriya wata irin kasa ce mai cike da abubuwan sha’awa, mamaki, takaici da tsoro. Wasu na yi mata kirarin: ramin kura daga ke sai ’ya’yanki. Wasu na kiranta: kasarmu ta gado.

Wasu na kallonta a matsayin hankaka mai mayar da dan wani nasa. A irin wannan yanayi ne mutane da yawa ke yi mana kallon tsuntsaye. Masu mulkinmu a cikin keji: ga ruwan sikari da tsabar hatsi da tsaro amma ba cikakkiyar kwanciyar hankali. Talakawanmu a sake cikin dajin Allah: ba takamaiman wurin samun abincin yau balle na gobe, ba tsaro, ba gata, amma da tabbataccen ’yancin watayawa a tsakanin dangi.

Saboda yanayinta na rikitar da tunanin mu¬tane cikin yadda take tafiyar da al’amuranta na yau da kullum, akwai jita-jitar tsohon Sakatar¬en Majalisar Dinkin Duniya, Mista Boutros Boutros Ghali Bamisire, ya taba yin ba’ar nuna shaukinsa na son zama a wannan kasa, idan wa’adin aikinsa a wannan majalisa mai alfarma ya cika. Kamar yadda aka ce, yawan cacar bakinmu da rashin afkawa cikin masifar da za mu kasa fitowa, a lokacin, sune abubuwan da suka kayatar da wancan dattijon difilomasiyya. Abin mamaki, daga gama shugabancin majal¬isar a Amerika sai Ghali ya waskewa kasarmu, ya nufi inda ya fi wayo. Ban ga laifinsa ba ko kadan.

Ko shakka babu Allah Madaukaki da Buwaya Ya albarkaci wannan kasa tamu da ni’imomi birjik: abinci, filin noma, teku, jama’a, ma’adinai, rashin mummunan yanayi ta fuskokin mahaukaciyar guguwa, aman wutar duwatsu, an¬nobar mutane da dabbobi, aikakken talauci da sauransu. Abubuwan da muke da su na fuskar nau’o’in abinci da kyakkawar kasar noma, idan wasu mutanen suka sami ushirinsu sai sun tsere kowa a duniya.

Misali, Isra’ila ba su da teku sai kogin da bai wuce matsayin kududdufi ba, ba su da wadatac¬ciyar kasa, ba su da kyawun muhalli ta fuskar noma, ba su da yawan jama’a, duk sabaninmu, amma yau bayan suna rike da kansu ta fuskoki da dama, akwai masu ganin da bazarsu duniya ke rawa. Babu ma’adinai, musamman fetur, a kasar Japan amma ya mutanenta suke?

Matsalolin Nijeriya sun hada da kasancewar mutanenta ba su damu da kyautata rayuwarsu ta muhimman hanyoyin da suka dace ba. Waye mai laifi a wannan yanayi? Talakawa ko masu mulkinsu? Ra’ayoyi sun kasu uku: masu mulki ne; talakawa ne; a’a su duka ne; kamar yad¬da na sha jin mutane na bayyana wa game da al’amarin. Menene gaskiyar magana?

Yabo ko zargi ga wani sashi ko jinsi na al’uma bisa ginshikin lalacewar wannan kasa yana kama da kwatancen giwar makafi: wanda ya shafa kafarta ya ce ta yi kama da bishiya; wanda ya shafa cikinta ya sifanta ta da rumbu; wanda ya shafa hancinta ya yi da’awar ta fi yanayi da mesa; wanda ya shafa kanta ya rantse giwa dutse ce. Waye mai gaskiya ko makaryaci a cikin wadannan makafi? Duk masu gaskiya ne bisa kuskuren fahimtarsu a dalilin gazawarsu ta ganin curarriyar siffar giwa. Kowannensu ya yi jawabin irin abin da Allah Ya sanar da shi. Ya ka¬sance mai gaskiya duk da amsarsa ba karbabbiya ba ce.

Kowane dan Nijeriya yana fusace da irin yanayin koma baya da kaskancin da muka samu kanmu a ciki. Kowa na son al’amura su gyaru. Kowa na neman mafita. Hanyoyin da za a bi don maganta matsalolinmu sun bambanta gwargwa¬don fahimtar, ko fasahar, ko ilimin, ko gaskiyar, ko hankalin, ko kidahumancin, ko duhun kan, ko jahilcin, ko son zuciyar, ko haukan wanda ke gabatar da nasa ra’ayin mafi kyawun hanyar ko dabarar da ya kamata a runguma don samun tab¬bataccen gyara.

Yau kam an yi amfani da sunan, ko ruhin, ko fahimtar, ko jahiltar tasirin manufofin siyasar addinanci, ko bangaranci, ko kabilanci wurin ne¬man mafita, da gaske ko da yaudara, ta irin wad-anan rikirkitattun hanyoyi. Tunani da yunkurin da suka haifar da kungiyoyi irin su Boko Haram, MEND, MOSOP, Ohaneze Ndigbo, OPC da sau¬ransu, a bangarorin wannan kasa da yin nazari ko la’akari da bukatu gami da manufofinsu, suna iya ba da damar duk sakarcin mutum ya fahimci inda ’ya’yan wadannnan kungiyoyi da matai¬makansu da iyayen gidansu suka sa gaba.

Shin gaskiya ne idan Nijeriya ta ruguje, tubalanta suka haifar da guntattakin kasashe gwargwadon yawan kabilunta, ko addinanta da rabe-raben kungiyoyinsu na cikin gida, za a fi samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da yalwataccen arzikin wadannan yuyuyun tara-gutsan gwamnatoci ko masarautun da masifar za ta wanzar? Me yake kawo bayyanannen rashin imani a tsarin zaman al’umar wannan kasa? Tsananin kishin addini ko gabarsa? Gasar kabi¬lanci ce? Adawar bangaranci ce? Bambancin akidar siyasa ne? Da wahala wani ya iya bayar da gamsasshiyar amsa ga wadannan muhimman tambayoyi. Me yasa?

Tabbas, gurbacewar hanyoyin da ake bi wurin kunsa cikin, kyankyasar, renonsu shuga¬banni da dasa su bisa muhimman kujerun mulkin al’uma na daya daga munanan illolin da ke gur¬gunta harkokin zaman lafiya gami da ci gaban Nijeriya. Babu inda wannan masifa ta yi katutu kamar a arewa. Jam’iyyun siyasa da wadanda suke samun tsayawa takarar manyan mukamai sun fi sha’awar samun mutane raunana, ko fasikai, ko maha’inta, a wurin tafiyar da sha’anin mulkin jama’a.

Misali, babu gwamnan da yake son mutumin da ya fi shi cancanta ya gaje shi? Babu gwamnan da yake taimakawa mutumin da ya san mutunci kansa, wanda ya fi kaunar kasa fiye da gwam¬nati ko kujerarsa, don ya zama wani abu. Duk da haka, har yau ban ga wani tsohon gwamnan are¬wa da ya gama lafiya da alakakai din da ya dora bisa al’uma ba. A mafiya yawan jihohinmu na arewa, kwamishina ko wani jami’in gwamnati ba ya zama dan gaban goshi sai ya kasance yana gwama aikin ofishinsa da dillanci, ko kawalci, ko ana wata masha’a ta hanyarsa ko da shi!

Mutanen Nijeriya mun fi kowa yawan ga¬batar da ayyukan addini duk da babu amana a tsakaninmu. Mun fi sauran kasashen Afrika yawan banza. Muna tafiyar da gwamnatocin mulkin siyasa a jihohi da tarayya da sunan di¬mokuradiyya, a karkashin jam’iyyu, yau shekaru goma sha hudu, duk da babu sahihancin zabuka tun farkon tsarin har zuwa yau. Jam’iyyar PDP ta haukace, ta bunkasa, ta allanta kanta, saboda rashin kafuwar tsarin bin doka da oda a kasarmu.

Muna ta ihu da zage-zagen neman sauyi ta fuskar jagorancin hadakar jam’iyyun mutanen da a kundinsu na siyasa sun sunnatawa kawun¬ansu zubar da jinin dimokuradiyyar cikin gida. Mutanen da suke amfani da gigicewar talakawa don su kasance karnukansu na farauta. Mutanen da suka dauka alfarma za su yi wa Nijeriya. Mu¬tanen da cin amanarsu da barnar gabobinsu suke rugugi a kunnuwan sauran jama’a har wannan ya hana kunnuwan jama’ar jin wa’azin da bakunan irin wadannan mutane ke furtawa!

Mafiya rinjayen mutanen da suke rike da muhimman mukaman mulki da tunanin wakilcin wata kabila, ko wani addini, ko wani bangare, a duk matakai, ba abin da yake gabansu daga sata, sai kwalliya, sai rinton wakilci, sai munafuncin yi wa ‘al’umarsu’ zagon kasa, sai kaskantar da siririn mutuncinsu, sai tsananin tumasanci, sai zaman kare a karofi, sai yaken banza da wofi!

Duk da gurbacewar Nijeriya, idan nan gaba irin wadannan ’ya’yan Allah-ba-ni suka zo da wata bukata, tasu ko ta wasunsu, tare da kokon bara, ya kamata wanda ya san kima da mutun¬cin kansa ya fatattake su. Irin wadannan ‘waki¬lai’ ko ‘shugabannin’ mutum-mutumi akwai su jingim a matakan kananan hukumomi da jihohi da tarayya. Ana iya samunsu a mukaman ‘zabe’ ko sauran mukaman nadi.

Sake rungumar irin wadannan butulu, sa¬karkarun munafukai, zai tabbatar wa da duniya dan Nijeriya bai san mutuncin kansa ba. Muna takure dalilan shigarmu munanan matsaloli, ko kallonsu da tabaron addinanci, bangaranci da kabilanci duk da kowa ya san karya ne. Dalili: yaudara ta zauna a zukatan ’yan Nijeriya, Da-ram! Dam!!

Domin martani, za a iya aiko da sakon imel ta: gadarrzare@yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here