KARAMAR HUKUMAR BATSARI: ABIN JIYA YA DAWO

0

KARAMAR HUKUMAR BATSARI: ABIN JIYA YA DAWO

Daga lawal iliya batsari
@ taskar labarai

Ga dukkan alamu tashe-tashen hankulan da Batsari ta yi fama da shi a watannin baya wanda aka samu saukinsu cikin wata guda daya gabata, yanzu hannun agogo na neman komawa baya, sakamakon yanda ‘yanbindiga da barayin shanu suka dawo da munanan ayyukansu a yankin inda a kowace rana zaka ji labarin kai hari da mamaye kauyuka. Inda akan samu hasarar rayuka da ta dukiya.

Ko a ranar 23/7/2019 wasu mahara sun kai hari a garuruwan Nahuta, Biya kikwana, da Garin waziri. A Garin waziri sun harbi mutum 1 a kafa mai suna Sada biri, a Biya kikwana sun yi garkuwa da matar aure mai suna A’isha, a Nahuta ma sunyi
garkuwa da mutum daya bayan sun sace dukiya da dabbobin yankin.

A ranar 24/7/2019 sun je safa inda suka kashe Mal. Shitu daga nan suka wuce Gobirawa inda suka sace shanu da tumaki, a Tsohuwar Ruma kuwa wasu da ba a san ko su wanene ba sun kashe Zubairu Makada ta hanyar saransa da adda.

See also  THE REPAIRS OF THE FAMOUS EKO BRIDGE IN LAGOS HAS COMMENCED!

A ranar 25/7/2019 barayi sun sake kai farmaki a Kasai a karo na 5 inda suka kashe Nura tare da sace dukiya mai
yawa.

A ranar 27/7/2019 wasu maharan sun sake kai hari a garin Manawa ta karamar hukumar Batsari suka harbe wani mai suna Dayyabu har lahira.

Sama da garuruwa 10 ne ‘yan bindigar suka tarwatsa kamar su Kasai, Nahuta, Madogara, Zamfarawa, Watangadiya, Batsarin Alhaji, Tashar Modibbo, Dumburawa,Yasore, Gobirawa, da Biya kikwana, Inda zakaga mata da tsofaffi dauke da yara da dan abinda yayi saura na kananan dabbobinsu nata shigowa cikin Batsari domin tsira da rayukansu, yanzu hakadai akwai dubban ‘yan gudunu hijira cikin garin na Batsari inda suke samun mafaka a gidajen ‘yan
uwa da abokan arziki.

Duk da wannan mawuyacin hali da suke ciki haryanzu babu wani tallafi daga karamar hukumar Batsari ko gwamnatin jihar Katsina ko wata magana mai dadi da aka yiwa ‘yan gudun hijirar. Dafatan Allah ya kawo masu dauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here