GASKIYAR ABINDA YA FARU A WAGINI

0

GASKIYAR ABINDA YA FARU A WAGINI

Lawal Iliyasu Garba
@ Taskar labarai and The links News

Ajiya talata 30/7/2019, da misalin karfe 5-30 na yamma barayin shanu akan babura 47 kowane dauke da goyon mutum 3, kamar yanda waniñ ganau yake shaida mana, da shigarsu garin suka cigaba da harbi sama wasu kuma na ci gaba da kama shanun jama’a, yayin da mutane ke cigaba da gudun tsira da rayukansu, suna zuwa garin Wagini, a nan ma barayin sun bisu har cikin garin na Wagini suna karbe shanu tare da cigaba da harbi a sama domin tsoratar da jama’a.

Jami’an tsaro sunkai dauki na gaggawa, an kona motar soja 3, an jima soja 2 rauni da danbanga 1, sai mutum 2 cikin jama’ar gari 1- Nafisu Danwanzan, 2-Hamisu Wagini.

See also  FG provides solar street lights, road to FCT communities

Yayin da dubban mutane suke tserewa daga gidajensu suna nufa Batsari domin tsira da rayukansu. Kafin harin na Wagini duk a ranar saida barayin suka fara kai hari a kauyukan Shekewa, Chambala, da ‘Yar laraba, da misalin karfe
4:00, na yammacin ranar talata. Yazuwa yanzu dai babu labarin rasa rayuka a cikin jama’ar gari ko ta jami’in tsaro, daga bangaren barayi kuwa Allah kadai yasan wadanda suka rasa rayukansu ko yawan masu raunuka bayan daukin da
jami’an tsaro suka kai, saboda suna tafiya da gawawwakin ‘yan uwansu da masu raunukansu.

Dafatan Allah ya tsare ya kiyaye gaba.
…………………………. …………………………………………….
Jaridar taskar labarai na a www.taskarlabarai.com The links news www.thelinksnews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here