YANTA ADDA SUN SAKE KASHE MUTUM UKKU A BATSARI

0

‘YANTA ADDA SUN SAKE KASHE MUTUM UKKU A BATSARI

Daga Lawal Iliyasu Batsari
@ taskar labarai and The links News

A cigaba da kai harehare da barayin shanu ke yi a karamar hukumar Batsari a rana 31/ 7/2019 wadda ta kasance rana ta hudu a jere, ajiya laraba barayin shanun sun kai hare-hare a yankuna da dama a karamar hukumar ta Batsari, da farko dai
sun kai hari a garin Labo, Bakon Zabo, Nahuta, Ajasu, da Zamfarawar Madogara.

A Bakon Zabo sun kashe mutum biyu sun jima hudu rauni
yanzu haka suna kwance a babbar asibitin Batsari suna karbar magani bayan sun yi awon gaba da shanun mutane, a Zamfarawa kuma wani yarone ya fada rijiya wajen gudun ceton ransa wanda ya zama sanadiyyar mutuwarsa nan take.

See also  Yan Sandan Sun Kama Likitan Bogi A Jihar Jigawa

A Nahuta kuma sun yi garkuwa da matan aure biyu, amma daga baya macce daya ta samu kubuta daga hannun ‘yan ta’addar. A garin Labo da Ajasu kuma sun yi awon gaba da
dabbobi da kaji da duk wani abu da su kaci karo
da shi mai amfani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here