ASALIN SHUGABAN KASAR BURTANIYA MUSULAMI NE Daga Taskar Labarai

0
416

ASALIN SHUGABAN KASAR BURTANIYA MUSULAMI NE

Daga Taskar Labarai

Wani rahoton da wani gidan talabijin din kasar Turkiya mai suna TRT world ya watsa a karshen satin da ya gabata shi, ya bayyana cewa asalin shugaban kasar Burtaniya na yanzu Boris Johnson musulmai ne da suka fito daga kasar Turkiya.

Shirin talabijin din na tsawon mintuna ukku, wanda duk mai bukatar ganin cikakken shirin yana iya ziyarar shafin Facebook na jaridar Taskar Labarai ko shafinsu na youtube.
A shirin an ce kakan kakan Boris Johnson ya fito ne daga wani gari mai suna Kalfat Beledeyesi a kasar Turkiya kuma har yanzu ginin asalin kakan nasu yana nan da kuma makabartar da aka rufe yan gidan zuriyar su.

Shirin yace wanda ya haifi kakansa mai suna Ahmad Riza Afendi an kashe shi a wajen fadan yakin neman ‘yancin kasar Turkiya. Shirin ya ci gaba da cewa kakansa na biyu mai suna Ali Kamayel shi ne wanda yayi gudun hijira a kasar Burtaniya.

Shirin ya cigaba da cewa Boris Johnson bai taba boye asalin sa ba cewa daga kasar Turkiya take ba inda har ya taba bakuncin yan asalin garin lnasu lokacin yana ministan Burtaniya. Ya dauki hoto dasu kuma ya nuna alfahari da ziyarar tasu.

Mutanen kasar Turkiya na Alfahari da murna dan asalin nasu ya zama shugaban kasar Burtaniya.


Gidan kakannin Boris Johnson a Turkiya


Garin na kakannisa
………………………………………………………………………..
Taskar labarai na bisa shafin www.taskarlabarai.com yar uwarta ta turanci kuma na bisa www.thelinksnews.com duk suna saman shafukan sada zumunta. 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here